Dakarun Bataliya ta 152 dake karkashin Operation Hadin Kai (OPHK), sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram shida a garin Banki da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno.
LEADERSHIP ta tattaro cewa an kashe maharan ne a ranar Lahadin da ta gabata a wani harin kwantan bauna da suka kai kan hanyar Kumshe zuwa Banki.
Wani kwararre a fagen yaki da ‘yan tada kayar baya, kuma masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, wanda ya tabbatar da harin, ya ce sojojin sun yi kwanton bauna ne bayan wani rahoton sirri da aka samu cewa an ga wasu ‘yan ta’addan Boko Haram da dama wadanda suka saba addabar matafiya tare da sace musu dukiyoyinsu a yankin.
Ayyukan sintiri da sojojin suka yi a kan titin sun samu babbar Nasara inda suka kashe kusan mutum shida daga cikin ‘yan ta’addan yayin da wasu da dama suka tsere da raunuka.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar 11 ga watan Oktoba, sojojin bataliya ta 21 da ke Bama karkashin Operation Hadin Kai (OPHK) sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram fiye da goma a hanyar Kumshe zuwa Banki.