Mutane 2 ne suka mutu, wasu uku sun jikkata bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari wata Cocin Celestial da ke bayan gidan man NNPC Mega dake unguwar Felele a Lokoja a jihar Kogi.
LEADERSHIP ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi.
Shedan gani da ido ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kutsa kai cikin cocin inda suka fara harbe-harbe ba kakkautawa.
Talla
Bayan tafiyar su, sai aka tabbatar da mutuwar mutane biyu nan take yayin da wasu kuma suka samu raunuka.
Wadanda suka samu raunukan a halin yanzu suna karbar kulawa a cibiyar kula da lafiya ta tarayya (FMC) da ke Lokoja.
Talla