Abubakar Muhammad Taheer" />

Rundunar ’Yan Sandan Jigawa Ta Cafke Mutum 27 Bisa Aikata Laifuka Daban-daban

Jami’in hulda da jama’a na Rundunar SP Abdu Jinjiri ya sanar da haka cikin sanarwar da ya bayar a nan Dutse.
Ya ce an cafke wadanda ake zargin ne bayan mukaddashin babban sufetan yan sanda na kasa Muhammad Abubakar ya kaddamar da shirin yaki da aikata miyagun laifuka da aka yiwa lakabi da operation puff adder.
SP Abdu Jinjiri ya ce biyu daga cikin wadanda ake zargi an kama su ne bisa zargin hada baki da yin garkuwa da mutane, kazalika an kama wasu da ake zargi da yin garkuwa da mutane bayan wasu ‘yan ta’adda sun kama Mista Adre Palsin dan kasar India da yake aiki a kamfanin gine-gine na Alren a yankin karamar hukumar Jahun a ranar sha takwas ga watan Maris da ya wuce.
Mai magana da yawun Rundunar yan sandan ya kara da cewa an kama ashirin da daya daga cikin mutanen bisa zargin aikata miyagun laifuka da fashi da makami a yankin karamar hukumar Dutse.
Rundunar ta samu Baburan sata guda uku daga wadanda ake zargi.

Exit mobile version