Rundunar ‘yansandan jihar Jigawa ta ce manyan jami’anta uku sun rasu a sakamakon rashin lafiya a cikin makonni biyu da suka gabata.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, DSP Lawan Shiisu, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin a Dutse.
- Mutum 2 Sun Mutu, An Kone Gidaje A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Jigawa
- Kanana Hukumomin Kano Da Jigawa 23 Na Kan Gaba Wajen Fuskantar Ambaliyar Ruwa – NEMA
Shiisu ya ce jami’an sun mutu ne a tsakanin ranar 22 ga watan Yuni zuwa 5 ga watan Yuli.
A cewarsa, waɗanda suka mutu sun hada da SP Salisu Salisu-Mudi daga Babura, wanda ya rasu a cibiyar lafiya ta tarayya da ke Katsina a ranar 22 ga watan Yuni.
Sai ASP Asabe Muhammad, shugaba na biyu a ofishin kula da jinsi na hukumar binciken manyan laifuka ta jihar (SCID), wanda ya rasu ranar Laraba.
Ya kara da cewa rundunar ta kuma rasa jami’in ‘yan sanda na Yankwaahi, CSP Muhammad Salihu-Koko, wanda ya rasu ranar Juma’a.
Shiisu ya ce, rundunar ta jajantawa iyalai da ‘yan uwan marigayin tare da addu’ar Allah ya jikansu da rahama.