Barkanku da kasancewa tare da shafin TASKIRA, shafin da ke tattaunawa game da abubuwan da suka shafi al’umma, wadanda suka hadar da zamantakewa na rayuwar yau da kullum, zaman aure, rayuwar soyayya, rayuwar matasa da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da irin kalubalen da wasu mazan ke fuskanta, na rashin samun girkin da suke son ci kullum a gidajensu, wanda matansu ba sa iya yi musu.
Da yawan Mata na iya kokarinsu wajen ganin sun inganta girkin maigida, sai dai rashin sa’a yayin da suka kai wa mazajen abinci sai su ki ci, sakamakon an dafa wanda zuciyarsu ba ta muradi. Ko me yake kawo hakan? Laifin waye tsakanin Mazan da Matan?, Me hakan zai iya haifarwa?, Ta wacce hanya za a magance matsalar?.
Dalilin hakan ya sa muka ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin inda suka bayyana nasu ra’ayoyin kamar haka:
Sunana Aisha Sani Abdullahi (Zayishatul Humaira) Marubuciyar Hausa Jos:
Wani sa’in laifin Mazan ne, domin su suke bawa matan damar dafa duk abin da suke son dafawa, wani ma ko da Matar ta nemi ya fadi abin da yake son ci zai tilasta mata da cewa kome ta dafa zai ci, idan kuma macen ta dafa wanda take ganin kamar shi ya ke so, ko zai so shi, yana zuwa zai ci in ya bude ya gani sai ya ce shi ba zai ci ba, ba shi yake son ci ba, alhalin shi ya ba ta damar dafa koma mene. Babu yadda za a yi mace ta dafa abincin da mijinta baya ci, sabida zama in yayi zama dole za ta gane wanne abu yake so wanne ne baya so?, sai dai idan daman ba ta iya girkin ba tun farko, ko kuma ba ta gane me mijinta yake so. Yana da kyau mazaje su zauna da matansu su fahimci juna, ta yadda za su rinka tattaunawa tsakaninsu game da abin da suke son dafawa, ba wai namiji ya ba da zabi ba karshe kuma ya ji haushin matar dan ta dafa abin da ta ga ya dace. Sannan su ma matan su rinka kokarin kulawa da mazan ko da namiji ya ba su zabi toh su zabi girkin da zai yi farin ciki da shi. Sannan Maza a rinka bawa mata kudi isasshe na cefane, sai ka samu girki me kyau me ma’ana, a wannan lokacin komai yayi tsada.
Sunana Ahmad Musa Senator daga Potiskum Jihar Yobe:
Toh! wannan laifin dai bana mata ko na miji ba ne, Laifin farko na iyaye ne, wasu iyayen ba su damu su nunawa ‘Ya’yansu yadda za su yi girki ba, wasu safe rana dare, an zo hutu, an tafi ‘lesson’ da sauransu, duk shi yake sawa yara ba su iya girki ba. Laifi na biyu gaskiya na mazaje ne, wani namijin yana bakin ciki yayyo cefane mai kyau a gidansa, ayi abinci me kyau, ga matar ta iya girkin amma kuma ya danyo cefanan ma da za a yi gwara ya je waje ya ci abinci ya bar matarsa da shinkafa da wake kawai. Toh! anan laifin mazaje ne, amma ‘Most important’ laifin iyaye ne tun farko gaskiya. Abin da hakan zai iya haifarwa shi ne; Namiji zai kara aure, musamman in mace ba ta iya girki ba. Hanyar da za a magance shi ne; Iyaye su tsaya akan ‘ya’yansu su koya musu girki. Shawarar da zan bayar ita ce; Namiji ya rinka kokari iya kokarinsa ya rinka yin cefane a gidansa me kyau, ba wai ya bar ta da shinkafa da wake ba ko Taliya da manja ko abin da yayi kama da haka, ya zamo yana cefane me kyau.
Sunana Yusuf Aliyu Kano:
Ni a ganina ai dukkan wani maigida ba a dora girki sai da saninsa, kuma shi yake cewa ga abin da yake so ake dorawa a gidansa, matukar maigidan ba soko bane, ma’ana wanda baya bawa iyalansa hakkinsu ta kowacce hanya. Da ma ba ci suke yi ba a gidan, ko ki ga ba su suke dawainiyar girkin ba. Wannan kuskure ne kawai ka fadi abin da kake so a girka ma ya fi.
Sunana Fadila Lamido Kaduna:
Ni a tunani na sai dai idan girkin ne matar ba ta iya sarrafashi yadda ya dace ba. Domin in da ace wadda baya so take yi tun kafin a yi nisa ya dace mace ta san abincin da mijinta ke so da wadda baya so. Bashi yiyuwa a ce kullum kin san mijin ki bai son kalar abincin har ya kai ga baya ci amma ki yi ta girkawa sai kace mara tunani. Kamata yayi idan namiji ya lura da matarshi ta kasa gane irin wadda ya ke so; sai ya daina bata zabi, duk da hakan ma bai cika faruwa ba gaskiya, dole mace ta san me ne mijin ta ya ke so meye baya so. Ni nafi ganin abin da zai sa namiji yaki cin abici a gida kawai babu dadi ne, wadda ya ke son ma ba a sarrafashi yadda ya dace ba. Akwai mata da yawa wadda haka suke, sai ka ga an cika hakkin cefane amman girkin babu dadi, wani cefanen da ba s cike hakkin sa ba wata macen ta sai ta sarrafa shi yayi dadi, a tunanina irin hakan rashin samun horo ne akan girkin tun daga gida, domin inda ace suna yi tun a gida anan za a gane matsala kuma a gyara mata tun kafin taje gidan mijin. Wannan kalubalai ne ga iyaye mata, ya dace ace kafin ‘yarki ta tafi gidan miji kin tabbatar da cewa ta iya sarrafa abinci. Rashi iya girki matsala ce babba, domin tun a farko mijin zai fara leken kwanon waje, kafin ya gaji ya fara tunanin kara aure, shawara ta anan da zaran kin kula mijinki baya cin abincinki sai ki yi kokari ki nemo hanyar gyara, idan kina girka waddda ba ya so ne ai ta kwana gidan sauki, sai ki gyara, domin abun takaici ne kwarai ace mijinki bai cin abincinki. Idan kuma sarrafawa ne baki iya yadda ya dace ba; toh gaskiya ki yi da gaske ki nemo wajen koyon girki tun kafin lamuran su cabe miki.
Sunana Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaki Jihar Kano:
Gaskiyar magana matsalar rashin iya girki ga mata ko kuma idan an dafa miji ya ki ci ya samo asali ne daga neman aure, Akwai wata ka’ida mai muhimmanci da ya kamata iyaye su lura da ita kafin aure shi ne. A zauna da bangarorin iyaye kowa ya fadi irin nau’in abincin da dansa ke so da wanda ba ya so, da nau’in kamshi ko wari domin ganin rayuwar auren su ta tafi cikin aminci. Kowa na da laifi a wannan bangare amma mace tafi laifi domin ita ya fi dacewa ta tambayi mai gidanta abincin da ya fi so. Tabbas zai iya haifar da namiji ya daina dawo wa gida wuri ya dinga yawon siyen abinci, da karshe dai zai kara aure domin huce haushi. Hanyar da za a magance hakan na amba ce ta a baya.. Idan kuma sai bayan aure matsalar ta faru to za a iya zama da iyaye domin bambance nau’in Dabi’u da abincin da ‘ya’yansu ke so da wanda ba su so.
Sunana Umar Muhammad Kontagora
Ni a ganina kamar babu fahimtar juna ne tsakanin ma’auratan, shi yake haifar da haka sannan shawarata anan ya kamata mata su yi abin da mazajensu ke so saboda rashin yin haka zai haifar da babbar matsla ga aurensu Shawarata kenan.
Sunana Rahma Sabo Usman daga Kano:
A ganina matan da ke girka abin da mazajansu ba sa so. Mostly su ke nemo kayan girkawar, ko kuma suke cefane. Hakan kan sanya matan ganin cewar ba kira, babu abin da zai ci gawayi. Don haka sai ta girka abin da ta san cewa zabinta ne, ko da kuwa mai gidanta ba ya so. Mostly laifin mazan ne. Gurin gaza sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.Yana matukar janyo tabarbarewar mu’amalar aure. Kowa ya dauki nauyin da Allah Ya dora masa, mai gida ya nemo abin da za a ci. Mace kuma ta sarrafa gwargwadan iko. Shawara ta Ke ‘yar’uwa mace ki sani cewar aure ibada ne, don mijinki bai da shi kar ki nemi hanyar wulakantashi ta hanyar yi masa horon yunwa. Kai kuma namiji ka sani duk macen da ka aura hakkinta yana wuyanka dole ka kula da ciyar da ita.
Nabeela Dikko daga Jihar Kebbi:
Abin da ke kawo hakan shi ne su mazajen sun fi jin dadin girkin waje, fiye da na cikin gida saboda an fi kashewa na wajen kudi, na gida kuwa sai ma uwargida ta cika kudin cefanan, dalilin da yasa ba sa jin ‘taste’ din girkin matayen su, wani zubin maccen ce ba ta iya girkin ba. Anan an yi hannun riga domin kowa na da laifi, idan har miji ya san tsakani da Allah ba ya kawo kayan da za ayi girki ya yi dadi,ko kuma yana laƙe hannu wurin ba da kudin cefane to maganar gaskiya shi kan shi ya san girki ba zai yi yadda ake so ba, sai mata da yawa wasu basu iya girki ba wannan ke sa maza basa son cin abimci, don haka idan kin san baki iya ba ki gyara, rashin hakan kuskure ne, wasu kuma sun iya tsabar son jiki ke sa ba sa yi sai dai mai aiki tayi to idan mijin baya so ba zai ci ba don haka anan kowa na da laifi. Hakan yana janyo matsaloli da dama wanda idan ba a fargaba auren ma zai iya lalacewa. Hanya daya ce maza da mata kowa ya gyara, idan matsalar kudi ko kayan abinci ne maza a dinga ƙwatantawa, mata a dage da koyon girki domin tallanki mutuncinki da darajarki da ƙimar ki ne. Shawara ta anan shi ne su zauna su fahimci juna, domin kawo gyara a zamansu.
Sunana A. Ibraheem daga Jihar Kano:
Sabida mazajen ba irin abincin ransu yake so ba, sannan laifin matane, laifin shi ne; basu iya ba ko ba a ko ya musu ba a gida. Laifin matane, abin da hakan Zai iya haifarwa shi ne; rashin zaman lafiya. Ta yadda za a maganace shi ne; zama da juna tare, wajan fahimtar da juna. Hanyar magance ta shi ne; hakuri da juna da kau da kai a wasu lokutan tunda idan za ka dinga kallon galibin kuskuran matarka ba za ka iya zama da ita ba shi ma idan za ki dinga kallon galibin kasawar mijinki ba za ki iya zama da shi ba.