Gagarabadon Majalisar Wakilai ta Kasa, Hon. Alhasan Ado Doguwa, ya yi bugun kirjin cewa, jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, APC, ta na da goyon bayan kashi 90 cikin 100 na yawan ’yan majalisarta kan batun zaben sababbin shugabannin majalisar.
Diguwa ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara sabuwar Masarautar Rano, domin yin mubayi’a ga sabon sarkin da a ka nada. A yayin da ya ke jawabi ga manema labarai, dan majalisar wakilan ya ce, dangane da sa-toka-sa-katsi da a ke yi a majalisar wakilai da ta dattawa kan zaben shugabannin majalisun guda biyu, su sama da kashi 90 cikin 100 sun amince da manufar jam’iyarsu ta APC da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da a zabi Hon. Femi Gbajabiamila, wanda ya fito daga jihar Lagos, don dai a samu daidaito da hada kan ’yan Najeriya wajen tafiyar da mulkin Najeriya, musamman idan a ka yi da la’akari da irin rawar da Yarabawa su ka taka a zaben APC da Buhari a 2015 da 2019.
Haka kuma sun amince da mataimakinsa ya fito daga yankin Arewa ta Tsakiya mai jihohin Nassarawa, Plateau, Benue, Niger, da Kogi kan dai wannan manufa ta APC da shugabanninta, don kauce wa matsalolin da a ka samu a shugabancin da ya gabata a majalisar.
Haka kuma sun amince da zaben Sanata Ahmad Lawan daga jihar Yobe a matsayin shugaban Majalisar Dattawa daidai da waccan manufar ta APC.
Sai kuma shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai da a ka ba Kano da Jigawa su fito da shi a majalisar wakilai, ’yan Jigawa sun yarda sun bar wa shi Hon. Doguwa.