Sabon Gwamna Jihar Gombe Ya Fara Nadin Mukamai

Gwamna Muhammad Yahaya na jihar ya tabbatar da nadin Farfesa Ibrahim Njodi, tsohon shugaban jami’ar Maiduguri, a matsayin Sakataren gwamnatin jihar.

Mohammed Umar, Daraktan gudanarwa da bangaren kudi, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi. Har wala yau sanarwar ta ce; gwamnan ya amince da nadin Bappayo Yahaya, a matsayin shugaban sashen ma’aikata, sia  Mohammed Kukandaka, a matsayin shugaban ma’aikata, sai Usman Kamara, a matsayin Sakataren PS.

Sannan an nada Ismaila Uba-Misilli a matsayin babban mai taimakawa gwamnan akan harkokin kafafen watsa labarai, da Kabiru Ibn Mohammad, Sulaiman Musa, Bintu Sunmonu da Jack Tasha, a matsayin mataimaka akan kafafen watsa labarai.

Sannan Musa Habibu (Bushasha) da Yakubu Ibrahim Sarki a matsayin mataimaka na musamman a yayin da Sani Garba ya kasance mataimaki.

Wannan nadin ya fara aiki ne nan take.

Exit mobile version