Kamfanin Dangote ya naɗa tsohon shugaban matatar mai ta Duqm a Oman, David Bird, a matsayin Shugaba (CEO) na farko da zai jagoranci sashen Mai da Sinadarai na kamfanin, domin magance ƙalubale da kuma ƙara haɓaka ayyukan matatar mai ta Lekki.
Bird, wanda ya fara aiki a watan Yuli 2025, ya ce zai mayar da hankali wajen ƙara tasirin kamfanin Dangote a ƙasashen Afrika gaba ɗaya, ba wai Nijeriya kaɗai ba. Ya ce zai tabbatar da samar da isasshen man fetur da kuma inganta aikin matatar Mai mai ƙarfin 650,000 b/d.
- Dalilin Da Ya Sa Dangote Ya Jinjina Wa Hukumar NPA
- Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka
Naɗin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin ke fama da wasu matsaloli da suka janyo tsaiko a ci gaban aiki. Tun bayan ƙaddamar da matatar a watan Janairun 2024, Dangote ya fara rage dogaro da shigo da fetur daga waje, yana mai zargin wasu ‘yan kasuwa da shigo da gurbataccen fetur da kawo cikas ga harkokinsu.
Bird ya ce zai yi amfani da ƙwarewarsa ta shugabancin matatar Duqm da sauya nau’in ɗanyen Mai da ake sarrafawa, wanda ya dace da tsarin da Dangote ke ƙoƙarin aiwatarwa yanzu. Kamfanin na shirin faɗaɗa matatar zuwa 700,000 b/d, da gina sabbin wuraren ajiya a Namibia da ƙasashe masu maƙwabtaka, da kuma ƙaddamar da motocin CNG guda 4,000 domin rarraba Man sa.
Aliko Dangote zai ci gaba da zama shugaban kamfanin, tare da niyyar fitar da hannun jarin sashen Man fetur a kasuwannin hada-hadar hannun jari na London da Lagos. Duk da ci gaban da aka samu, matsaloli a babbar na’urar RFCC sun rage yawan Man da ake fitarwa a 2025, inda yanzu yawancin fitar da Mai daga matatar ya ta’allaƙa ne da jirgin sama (jet fuel) da Gasoil.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp