A ranar Litinin ne ‘yan bindiga suka samu nasarar kai hari a Makaratar Sakandare ‘yan mata da ke a garin Maga a karamar hukumar mulki ta Danko Wasagu a Jihar Kebbi, inda Suka yi awon gaba da ‘ya matan guda Ashirin da biyar da kuma harbe wani malami mai suna Malam Hassan Makuku.
Wakilinmu ya samu zanta wa da Matar mariyayin, inda ta bayyana yadda ‘ Yan bindigar Suka Kashe Mijinata yayin da Suka kawo hari a Makaratar Sakandare ta ‘yan mata Kafin samun nasarar yin awon gaba da ‘ya matan. Ta ce” a daren ranar lahadi da misalin karfe 2 zuwa 4 na asuba wayewar safiyar litinin ne ‘yan bingida Suka shigo Makaratar ta Maga, inda Suka fara yada zango a gidanmu a cikin Makaratar, naji alamar motsin bude kofa shigowa gidan sai na tada mijin nawa Malam Hassan Makuku cewa ya tashi ga awaki nan sun bude kofar gida domin kada suyi muna barna, ashe ‘yan bingida ne.
- Sai An Magance Cin Hanci Da Rashawa Nijeriya Za Ta Zauna Lafiya – Masani
- Rukunin Ba Da Tallafin Jinya Na Sin Da Asibitin Nijar Sun Gudanar Da Aikin Jinya Kyauta
” Muna tada kai sai kawai muka gan mutane kewaye da mu da bingigoginsu, inda suke sanye da tufafi irin na soje kuma yaren Fulani suke yi. Sai suka cewa maigidana ya gwada musu inda ‘yan Makaratar ke kwana, sai ya basu amsar cewa bai sani ba, daga nan kawai sai daya daga cikinsu ya halba bingigarsa zuwa ga jikin maigidana yayin da naga zai fadi sai na tashi da nufin na tallabe shi, sai suka daka mani tsawa cewa idan na tallaba shi zasu harbe ni.
Daga nan sai ban taba shi ba, nima suka cewa sai na shiga gaba in gwada musu inda ‘yan Makaratar ke kwana, muna cikin hakan sai kawai Suka ji tashin yara daga nan sai suka aukawa ‘yan Makaratar, Kafin a samu dauki daga mutane ko jami’an tsaro sun samu nasarar awon gaba da ‘ya matan guda Ashirin da biyar kamar yadda bayyanai Suka nuna a hukumance, Inji Amina Hassan Makuku”.
Bayan an dauki lokaci, sai ga jama’ar gari da jami’an tsaro, Amma a lokacin sun samu nasarar awon gaba da ‘ya matan. Bayan na dawo cikin hayyacina a lokacin ne na iya bada labarin yadda suka harbe Mijina. Kazalika sai ga tawagar mataimakin Gwamna ya shigo Makaratar bayan samu labarin abin da ya faru a Makaratar. Bayan daukar wani lokaci sai kuma maigirma Gwamnan Jihar Daktar Nasir Idris tare da wasu mutane ya shigo, Wanda muka samu labarin cewa ko da wannan matsala ta samu baya a gari yana Abuja, Amma anan take ya shigo jirgi zuwa Makaratar garin Maga don jajanta muna kan irin abin da ya same mu.
Bayan ya kammala zagayawa ya kuma gana damu da sauran uwayen ‘yan makaratar, inda ya tabbatar muna da cewa gwamnati za ta dauki duk matakin da ya dace domin tabbatar da cewa an ceto wannan yaran.
Har ilayau, Amina Hassan Makuku ta kara da cewa” Mijina Malam Hassan Makuku malami ne a wannan Makaratar haka kuma shi ne ke kula da harakokin tsaron Makaratar Kafin ‘yan bingida kuka Kashe shi.
Har ilayau wakilinamu ya zanta da wani mai suna Lawal Altine, mahaifin dalibai uku a makarantar, inda ya ce” muna jiran muji labarin cewa an ceto muna yaranmu matan da ‘yan bingida suka yi awon gaba dasu,In ji shi”. Ya ci gaba da cewa “Daya daga cikin ‘ya’yana mata, Khadija ‘yan aji shida ce, Allah ya tsare ta ta hanyar boyewa a bayan gida. Ta yi sa a, ba ta damu da duk harbe harben da ‘yar bingidar suka yi tayi ba, har sai da suka yi awon gaba da ‘yar uwanta bayan su wuce sannan ta fito dag bayan gida ta bature ke kira toilet, In ji shi “. Wani labarin da nake bayyanawa abin da Khadija ta bayyana ne yayin da mu uwaye muka samu labarin abin da ke faru sannan muka shigo Makaratar.
“Muna cikin tashin hankali da fargaba bisa ga halin da muke ciki a halin yanzu. Amma da yake mai girma Gwamnan Jihar Daktar Nasir Idris ya bamu tabbacin ceto muna yaranmu zamu dan ji dama. In ji shi.
Wani mahaifin, Fatima Ibrahim, ya bayyana cewa “Ina so gwamnati ta taimakamu wajen ganin an gwaggata ceto muna yaranmu tun ‘yan bingida basu hallakasu ba, inji shi.
Saboda haka, muna rokon Allah ya dawo muna da yaranmu cikin koshin lafya ba tare da wata matsala ba.
A nashi jawabi ga uwayen yaran da aka sace, Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya ziyarci makarantar kuma ya hadu da iyayen matan da aka sace, ya basu tabbatacin cewa duk abin da zai yiwu za a yi don tabbatar da cewa an ceto wadannan yaran, Inji shi”.
Hukumomin tsaro sun sha alwashi tabbatar da cewa sun gudanar aikin ba dare ba rana don ganin cewa sun ceto wadannan yaran. Hakan kuma za su gudanar da aikin hadin gwiwa tare da ‘yan sanda, sojoji, da kuma jami’an ‘yan banga da aka turo a yankin don tabbatar da cewa an ceto wadannan yaran da aka sace.
Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, Janar Waifi Shibu, ya ba da umarni ga jami’an sojoji na tabbatar da sun kara kwazo da inganta kokarinu wajen ganin cewa an ceto ‘yan matan, za mu tabbatar da cewa wadannan ‘yan matan Makaratar Sakandare ta Maga sun dawo ga hannun uwayensu cikin koshin lafiya, In ji shi”.
Al’ummar garin Maga sun faru gudanar da addu’o’i na musamman don ganin cewa Allah karbi addu’arsu don samun nasarar ceto wadannan yaran.














