Sabon mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Frank Lampard ya ce baya jin za’a magance matsalar Chelsea a rana daya, bayan da ya fara da kafar hagu a Wolberhampton.
Lampard wanda ya ja ragamar Chelsea a karon farko a matakin rikon kwarya, ya yi rashin nasara 1-0 a gidan Wolbes a wasan mako na 30 a Premier ranar Asabar a filin wasa na Moulined.
- Wang Yi Da Qin Gang Sun Gana Da Ministar Harkokin Wajen Jamus
- Kin Amincewa Da Kwangilar Dala Miliyan 22 Ta Yi Sanadiyyar Sauke Ni Daga Shugabancin NPA –Hajiya Hadiza Bala-Usman
Wasan farko da ya shugabancin Chelsea tun bayan watanni 27 da aka kore shi a Stamford Bridge, Thomas Tuchel ya maye gurbinsa wanda shi ma daga baya aka kore shi.
Chelsea ta kasa zura kwallo a raga a wasanni uku a jere kenan, karo na 11 da aka doke ta a babbar gasar firimiyar Ingila ta kakar nan wanda hakan ba karamin ci baya bane ga kungiyar.
”Mun kwana da sani ba ma yanayi mai kyau, ba wanda muke bukata bane, amma da akwai dalilin hakan ban jin zan warware matsalar nan a kwana daya, dole sai mun kara kwazo a wasa da sa kaimi.” In ji Lampard.
Wasa hudu kenan da Chelsea ba ta yi nasara ba, wadda a ranar Laraba ta je gidan Real Madrid, domin buga Champions League kuma a sati mai zuwa kungiyoyin za su sake karawa a filin wasa na Stamford Bridge.
Lampard, wanda bai da kungiya tun bayan da Eberton ta sallame shi a watan Janairun 2023, ya horar da Chelsea daga watan Yulin 2019 zuwa Janairun 2021 daga nan ta kore shi.
An nada shi kociyan rikon kwarya zuwa karshen kakar nan a makon nan, bayan da Chelsea ta kori Graham Potter a karshen watan daya gabata, wanda ya yi watanni bakwai kacal yana koyar da kungiyar.
Tun farko Chelsea ta sa Potter ya yi murabus daga aikin Brighton, sannan ta kulla yarjejeniyar shekara biyar da shi saboda rashin tabuka abin arziki ya sa kungiyar ta sallame shi.
Lampard ya buga wa Chelsea wasa a Stamford Bridge lokacin da Roberto di Matteo ya ja ragamar kungiyar ta lashe Champions League a 2012 a matakin rikon kwarya daga baya aka bashi jan ragama.