Sai Matasa Sun Samu Aikin Yi Za Mu Yarda Da Tattalin Arziki Ya Farfado —Salihu Halliru

Daga A. A. Masagala, Benin

Wani Dankasuwa a lokaci guda kuma jagoran Babbar kasuwar Raguna da awaki ta Benin jihar Edo Alhaji Salihu Halliru ya yaba wa gwamnati mai ci kuma ya kalu bance ta a cikin bayaninsa da ya yi a karshe inda ya fara da ce wa: ‘’Lallai ne a sanin kowa matukar za a yi gyara dole ne a fuskanci wasu matsaloli wadanda idan aka yi hakuri sai ka gani a karshe ana jin dadi.

Kuma sai ya kara da ce wa: ‘’A hakikanin gaskiya mun san kafin wannan gwamnatin kasar nan ta fada cikin matsalar rashin tsaro da ta tattalin arziki shi ne ya sa muke ganin matsalolin suka ci gaba da hayayyafa nan da can har ya kai muke fama da wannan tsadar rayuwar amman yanzu da alamar kome zai yi sauki.

Alhaji Halliru ya ci gaba da cewa, wasu mutane suna tunanin ce wa ko siyasa ce ta kawo haka wasu kuma suna tunanin kabilanci ne amma ni a fahimtar da na yi wa halin da muke ciki babu batun siyasa ko kabilanci a ce su ne suka janyo mana wadannan matsalolin ba ni a ganina shi ne yaki da kungiyar Boko-haram ne ya jefa kasar nan cikin halin ni-ya’su domin irin kudaden da gwamnati ta ci gaba da kashewa na yaki da su domin dakile su na tsawan lokaci a yayin da kasa take fama da dukushewar tattalin arziki daga wancan lokatan baya kawo yanzu.         Gwamnati ta kada gangar cewa tattalin arzikin kasa ya farfado mun ji wannan bayanin amma kuma ba za mu yarda da tattalin arzikin ya farfado ba har sai mungani matasa sun samu ayyukan yi a duk fadin kasar nan don haka irin shawarar da zan bai wa ita gwamnatin tarayya domin magance matsalolinmu a kasar nan ita ce ta samar wa matasa aikin yi tare kuma da gina kamfuna da masana’antu a cikin jahohin kasar kuma gwamnati ta tsananta dokar hana ‘yan siyasa da masu hannu da shune tattara dukiyarmu suna kai su boye a kasashen waje kuma ya dace a ce gwamnati kasar nan ta bari a ci gaba da shigo da abinci bayan abin da muka nomawa domin hakan zai kara samar da saukin farashin abinci ba kamar yadda wasu marasa imani suke tunani ba kuma gwamnatin ta tallafawa manoma da kudade da sauran kayan aiki na zamani domin ta hakan zai sa a samu a bunkasa harkar noma a kasar nan.

Dan kasuwa Alhaji Halliru ya kara da bayanin cewa: ’’Kamar yadda gwamnatin take bukatar a koma gona sai ta yi misali da kanta kama daga ita gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi suma su koma su dukufa a kan harkar noman kamar yadda manyan kasashe shugabanninsu da attajiransu da ‘yan siyasansu suke yi domin yin wannan babu shakka zai kawo yelwatar abinci tare da farfado da tattalin arziki wanda kullum ake zagaya wuri guda ba gusawa”.

Daga nan kuma sai Alhaji Halliru ya juya a kan ‘yan uwansa ‘yan kasuwa ya shawarce su da cewa: ‘’Ya zama wajibi kowane  dan kasuwa a kasar nan ya rike gaskiya ya ci gaba da kasuwanci tare kuma da mayar da hankali a kan harkar noma na damuna ko na rani da wannan sai mu ga kome ya yi mana sauki a kasarmu Najeriya.” Inji shi’.

Exit mobile version