Abdullahi Muhammad Sheka" />

Sai Mun Tabbatar Da Kayar Da Dan takarar Gwamna A PDP A Kano –Hon. Umar Yusif

UMAR YUSIF UMAR Kashe Kobo shi ne Manajan Daraktan Hukumar Gidan Adana Namun daji na Zoo da kuma lura da dajin Falgore, sannan kuma shugaban Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano, Tsohon Malamin Makaranta gogaggen masani ta fuskar addinin Musulunci. A Tattaunawarsa da Wakilinmu a Kano ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, Kashe Kobo ya bayyana yadda yaji da kuma yadda ya tsinci kansa lokacin da aka ambata shi a matsayin shuganan wannan gida na Zoo, sannan kuma ya bayyana yadda za su yiwa Jam’iyyar PDP da dan takararta a matsayin gwamnan Jihar Kano yan kaunar da yace a kwatun da Abba Kabir ke zabe sai sun ka dashi, ga dai yadda tattaunawar ta kasance:

Da farko Za muso Ka gabatarwa da Mai Karatu kanka da kanka?
Alhamdulillahi Sunana Umar Yusif Umar Kashe Kobo Shugaban Gidan Adana Namun daji na Zoo da kuma lura da dajin Falgore, sannan kuma shugaban Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano.

Wane Hali aka samu gidan Adana Namun dajin zuwanka?
Alhamdulillahi muna kara godiya ga Allah madaukakin sarki, babu shakka tun daga lokacin da Gwamna Ganduje ya amince da na zama shugaban wannan gida a ranar 22/10/2018 na samu wannan gida da dukkan abubuwan da ya kamata gwargwadon iko, ga daraktoci nan guda hudu da sauran ma’aikata tun daga kan manya har zuwa kan kanana da ma wadanda suke tsarin biya kullum kullum.
Sannan kuma akwai dabbobi iri daban daban har guda 279 da kaloli kusan kala 65 wadanda wasu ke ruwa, kan tudu da tsintsaye iri daban daban. Kamar yadda aka sani tsohon Gwamnan Kano Audu Bako ne ya sa harsashin ginin wannan gida a shekara ta 1971 sannan kuma gidan ya zama hukuma mai zaman Kanta a shekara ta 1999. An kafa wannan gida kan wasu abubuwa guda hudu, ilimantarwa, bincike da kuma yawon bude ido. Wannan gida ya na kuma lura da dajin fargore mai fadin kadada kusa 920 akwai cikakkun ma’aikata, ma’aikatan wucin gadi da kuma masu aikin sa kai. A kwai kuma bagarorin lura da lafiyar dabbobi wanda keda likiti sukutum wanda ke lura da wannan bangare.

Ba ya ga namun daji shin ko akwai wasu abubawa da ake gudanarwa a wannan gida?
Kwarai da gaske akwai bangaren da ake gudanar da harkokin al’adunmu na gargajiya musamman koroso, da wuraren gudanar da harkokin bukukuwa wanda aka tanadi wuri da abubuwa zama wanda zai dauki mutun 200 sai kuma wanda basu kai wannan ba suna daukar mutane 100-150,sannan kuma an samar da tsarin mai kyau domin tabbatar da kare kimar addininmu da al’adunu. Saboda haka wadannan sune wasu daga cikin abubuwan da na iske a wannan gida, dasu kuma muke ci gaba da ayyuka akansu domin tabbatar da cigaban da ake bukata.

Ya ya ake gudanar da shugabancin wannan gida domin kamar yadda ka ambata wuri ne mai maban bantan abubuwa iri daba daban?
Gaskiya kamar yadda aka sani ni tsohon malamin makaranta ne, na koyar a islamiyya na koyar amakarantun firamare, na zama Akanta saboda haka ina da gogewa ta fuskar aiwatar da irin wannan aiki, hakan ya sa kullum idan na shigo wannan gida sai na zaga cikin gidan domin duba halin da namun daji ke ciki, domin amana ce a ka damka min, kamar yadda tarihi ya nuna yadda Allah ya yi rahama ga wata mata karuwa sakamakon shayar da kare ruwa, ina kuma gare ni da Allah ya damka manar dabbobi a hannuna, kuma na tabbatar da cewa sai Allah ya tambayeni. Ina tabbatar maka da cewa lokacin da aka damkan wannan amana har sai da na fashe da kuka domin na tabbatar da cewa aiki ne babba.
Saboda haka ko da ranar lahadi sai na shigo wannan gida sannan kuma ina yin kokari wajen tabbatar da cigaban kananan ma’aikata wanda da farko na fara da samar masu da Uniform tare da samar masu kayan aiki kama daga fitilar aiki da kuma kayan da za su taimaka masu wajen gudanar da ayyukansu. na yi kokarin gyara wani kejin ajiyar Dorinar ruwa wanda na hangi rashin kyan shigen na iya zama barazana, haka kuma na gyara wata rumfar ajiyar motocin shugabanni inda muka kashe makudan kudade akan wannan aiki. Haka bangaren likita na tarar babu makewayi a wurin tuni na sa aka fara aikin samar da wurin kewayawa domin amfanin likotocin dake aiki a wannan bangare, haka lamarin yake a bangaren asibitin mata shima muna ta aikin gyara shi domun yin daidai da bukatun al’umma.
Wani abin sha’awa kamar yadda aka sani a kwanakin nan anji yadda akayi ta yada zantuka cewar an mayar da wata mace kura, to ahalin yanzu duk da wannan lamari ba haka ya ke ba, amma dai kurar na nan a hannun mu mun killace ta kuma ana ci gaba da bincike, idan kotu ta gama dashi mai wasa kurar to mu kuma zamu duba mu tabbatar da ya na da lasisin amfani da kurar, idan yana dashi sai mu bashi kayansa, idan kuma bashi da lasisi lallai zamu tabbatar da adabtar dashi da yin duk abin da ya kamata.
Akwai hukumar dake lura da harkokin gidajen adana namun daji ta Duniya wadda abaya ta gamsu da matsayin wannan gida, shin har yanzu wannan gida na rike da wannan kambu?
Ina tabbatar maka da cewa duk fadin Najeriya babu wani gidan adana namun daji da yakai na Kano, Jihar Kano kadai keda gidan zoo kuma take da dajin Falgore, ko a ‘yan kwanakin nan na ziyarci dajin falgore na ziyarci Jami’in ‘yan sandan wannan yanki na kuma ziyarci alkalin da kewannan bangare da kuma dagatan dake wannan yanki, saboda haka ina tabbatar maka Wannan gida har yanzu shike rike da wannan Kambu kuma zamu ci gaba yin duk mai yiwuwa domin kare wannan kambu.

Ya Danganta ka take tsakanin ka da ma’aikatan wannan gida?
Alhamdulillahi kamar yadda na fara ambatawa tun da farko akwai kyakkyawar danganta tsakanina da ma’aikatan wannan gida tun daga kan manyan ma’aikata har zuwa kasa, domin lokacin da na shigo wannan gida da kananan ma’aikata na fara zama na saurari matsalolinsu sannan kuma na zauna da manyan ma’aikata. Na fada maka akwai bangarori hudu wanda kuma kowanne akwai darakta dake kula da sashin kuma alhamdulillahi ba abin da zace dasu sai godiya domin suna bani hadin kai kwarai da gaske.
Mene sakonka na karshe?
Sakona ga al’umma Jihar Kano shi ne zabe ya rage kwanaki tara saboda haka kowa idan ya yi sallah ya roka mana Allah fatan ayi wannan zabe lafiya a gama lafiya, Allah ya tabbatarwa shugaba Muhammadu Buhari mulki karo na biyu da Gwamna Ganduje, domin kaubalen dake cikin wannan zabe ya wuce maganar siyasa kalubalen wannan zabe ya fi na 2015, wannan zabe so ake a dauki mulki a baiwa PDP wanda dan Arewa sai ya gwammace kida da Karatu, idan ka kalli Atiku ka dubi wanda ya dauko a matsayin mataimakinsa, idan mulki ya kubuce ya koma hannun wadancan mutanen sai dan arewa ya yi kuka da idonsa.
Saboda haka muna kara godiya da jinjina ga Gwamnan mu mai adalci da shugaban Jam’iyyar APC bisa irin jajircewarsu wajen ganin an hidinmatawa talakawan Jihar Kano, wannan tasa ya zama wajibi jama’a mu yaba kyauta da tukuici a lokacin zabe mu fito kwanmu da kwarkwarta mu yiwa Jam’iyyar APC luguden kuri’a daga sama har kasa.

Exit mobile version