ÆŠan wasan gaban Arsenal, Bukayo Saka, ba zai iya buga wasan Arsenal da Liverpool na ranar Lahadi ba sakamakon raunin da ya samu.
Haka kuma ba zai buga wasannin da ƙasarsa ta Ingila za ta yi da Andorra da Serbia da za a yi watan gobe ba.
- Ranar Hausa Ta Duniya: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka
- An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing
Saka mai shekaru 23 ya ji rauni a ƙafarsa a wasan da suka doke Leeds United a ranar Asabar, kuma likitoci sun ce zai ɗauki aƙalla makonni huɗu kafin ya dawo filin wasa.
Haka nan akwai shakku kan ko Martin Odegaard, kyaftin ɗin Arsenal, zai buga wasan Liverpool a filin Anfield.
Shi ma ya samu rauni a kafaÉ—arsa a wasan da Arsenal ta doke Leeds da ci, inda kocin Arsenal Mikel Arteta ya cire shi a minti na 38.
Har yanzu babu tabbaci ko zai iya buga wasan.
Arsenal na fatan cewa Saka da Odegaard ba za su daÉ—e suna jinya ba.
A kakar da ta wuce, Saka ya sha fama da rauni har ya yi watanni uku ba ya wasa.
Sai dai a bana Arsenal ta ƙara wasu sababbin ‘yan wassan gaba kamar Viktor Gyokeres da Eberechi Eze, baya ga waɗanda ta ke da su kamar Gabriel Martinelli, Leandro Trossard, Ethan Nwaneri da Max Dowman don rage giɓin Saka da Odegaard.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp