Sakacin kamar yadda kowa ya sani wata kalma ce da take nufin ko nuna irin rikon sakainar kashi da akan yi ma wani al’amari,idan ba sa’a aka yi abin daga karshe ba zai haifar da da mai ido ba a gaba.
Duk irin nuna halin ko in kula kan nal’amuransu, shi yake sa yake har a samu gungun wasu matasa yanzu wadanda tun lokacin suna kananan yara ne aka yi watsi da su.
- Za Mu Iya Ciyar Da Kifayen Da Muke Kiwo Da Mushe?
- A Yayin Bikin Tsakiyar Yanayin Kaka Xi Jinping Ya Bayyana Muhimmancin Iyalai
Wannan watsi dasu wanda kamar yadda na yi bayani a makon daya gabata shi yake sa wa idan suka fara girma sune suke zabarwa kansu abinda ya dace su yi,da kuma suke ganin zai fidda su halin da suka tsinci kansu.
Masu iya magana sun ce da digon ruwa a hankali watarana sai wuri ya zama Kogi tun yana Korama, idan har wancan Maigida da makwabtansu Magidanta shi da su, suka kasance basu yi ma ‘ya’yansu tarbiyar data kamata,da zata taimaka masu a gaba,suma su taimakawa kansu da wasu ba su kasance cima- zaune ba.
Maganar gaskiya wani Maigidancin ko Kajin ma da yake kiwo da Dabbobi bai damu da basu kulawa ba, ko samar masu wurin da zai kiwata su a gidan shi.
Ranar daya bukaci kudi zai ce a ina Kajin ko Dabbobin suke kwana,aje a kamu su domin zai kai su kasuwa ya sayar.
Wanda bai iya kulawa da Kaji ko Dabbobi ba ta yaya zai kula da bayar da tarbiyya maikyau ga ‘ya’yansa?
Irin wadannan ‘ya’yan da ya dace ace tun farko an fara sa su a hanyar data dace, amma sai aka yi watsi dasu,cikin sauki irinsu sune idan suka kai ga zama bata –gari sune akan yi amfani da su wajen aikata laifuka dabandabanHanya mafita ita ce kowanne Maigida ya rika yin abinda ya dace wajen sa ‘ya’yanshi farawa da zuwa kan hanyar da zata kai su zuwa Tudun- Muntsira.