Rabiu Ali Indabawa" />

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Isa Gabas Ta Tsakiya

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya isa kasar Saudiyya, inda ya fara ziyarar kwanaki uku a yankin gabas ta tsakiya, wadda a cikinta zai ziyarci kasashen Jordan da Isra’ila.

Ana sa ran ziyarar ta Mike Pompeo zata mayar da da hankali ne a kan yarjejeniyar nukuliyar Iran, wadda shugaban Amurka Donald Trump ke fatan a yiwa garambawul.

A farkon shekarar da muke ciki ne kuma Trump ya yi barazanar janye Amurka daga yarejejeniyar, muddin ba a sauya mata fasali ba, nan da zuwa 12 ga watan Mayu.

Kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliyar Iran a shekarar 2015, sun hada da Birtaniya da Faransa da Jamus da Rasha da kuma China.

Ra’ayin baki dayan kasashen ya ci karo da na Amurka da ke neman a sake fasalta yarjejeniyar, kudurin da itama kasar Iran ta ci alwashin ba zata lamunci kyale aiwatar da shi ba.

 

Exit mobile version