Biyo bayan sanarwar da Gwamnatin Tarayya na a sake bude iyakokin Nijeriya hudu na kan tudu da Gwamnatin ta sa aka garme a watannin baya, bincike ya nuna cewa, ayyukan boye abinci ya ragu matuka a kasuwannin jihar Katsina.
Bugu da kari, sanarwar ta kuma zo wa, manyan ‘yan kasuwar sayar da hatsi da su ke fake wa da wasu ‘yan na kama wajen sayen hatsin da ya wa su kuma boye shi domin samun kazamar riba a gaba.
A cewar wasu dilolin hatsi, duk hana shigo da shinkafa da wasu amfanin gona cikin kasar, wasu nanyan ‘yan kasuwar sun kasance su na jin tsoro ganin cewa, ako wanne lokaci, gwamnatin za ta iya canza ra’ayinta.
Wani bababban dan kasuwar hatsi Alhaji Aminu Hussain ya ce, boye hasti ba wai sabon abu ba ne a kasuwanni, sai dai, lamarin ya karu ne saboda da sababbin tsari da Gwamnati mai ci ta samar da kuma kulle iyakokin kasar nan.
Wani dilan hatsi Mallam Muhammadu Tarzana, a kasuwar Bakori sanarwar ta yi tasiri kan farashin manyan kayan masarufi a kasuwar sabanin shekarar da ta wuce, inda a daidai wannan lokacin, ake sayar da masara daga Naira 8,000 zuwa Naira 9,500, sai kuma sorghum kan Naira 7,000, da a yanzu, ake sayar wa daga Naira 14,000 zuwa Naira 13,000.
Ya ce, sanarwar ta sa farashin buhun Shinkafa ta cikin gida ya ragu daga Naira 14,000 zuwa Naira 12,000, Rogo kuma daga Naira 14,500 zuwa Naira 13,000, inda kuma buhun Masara daga Naira 15,500 zuwa Naira 14,000, inda ya ci gaba da cewa, akasarin manyan ‘yan kasuwar sun janye daga sayen hatsin mai dimbin ya wa, bayan an yi sanarwar.
Sai dai, ra’ayin wasu ‘yan kasar ya banbanta kan sake bude iyakokin da aka yi, inda akasarin manoman a kasar da kuma ‘yan kasuwar sun fi son a ci gaba da barin iyakon a kulle, musamman saboda da dimbin ribar da su ke samu.
Su kuwa masu saye, sun yi maraba da wannan matakin na bude iyakokin, musamman domin su samu saukin sayen kayan abinci, musamman Shinkafa.
Sai dai, murnar ‘yan kasar ta koma ciki, ganin cewa, shinkafa, kajin gidan gona, man girki na waje da sauransu, har yanzu na daga cikin jeren haramtattun kaya da ta hana shigo wa da su cikin kasar.
Wani kwarre a fannin aikin noma Sani Mu’azu Hunkuyi ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ka da ta ja da baya, ya ce, gwamnatin ta zuba dimbin jari a fannin aikin noma a saboda haka, bai kamata a bar hakan ya durkushe ta hanyar bayar da damar shigo da kaya cikin kasar nan ba .
Mu’azu ya ci gaba da cewa, “ Kwarai da gaske ne akwai jin tsoron karancin abinci a kasar, amma za a iya magance hakan ne ta hanyar mayar da hanakali wajen noman rani, amma barin a ci gaba da shigo da kaya cikin kasar, zai kara zafin matsin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a yanzu kuma hakan, zai yi wa tsare-tsare da shirye-shiryen aikin noma na Gwamnatin Tarayya”.