Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sauya fasalin naira ya yi matukar taimaka wa wajen samar da ingataccen zabe a 2023.
Ya kuma bayyana dalilin da ya sa bai kori tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele duk da an alakanta shi da neman tikitin takarar shugaban kasa a APC a 2023.
- Jihar Kaduna Za Ta Ƙarfafa Ƙawancen Tattalin Arziki Da Ƙasar Jamus
- Sin Ta Riga Ta Bayar Da Gudunmawar Da Ake Bukata Ga Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya
A cewarsa, ba zai iya korar Emefiele daga ofis ba saboda bai fada masa burinsa ba na neman shugaban Nijeriya ba.
Buhari ya bayyana hakan ne a wurin kaddamar da littafin ayyukan da ya yi tun daga 2015 zuwa 2023, wanda tsohon mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya rubuta.
An dai kaddamar da littafin ne a hukumance a Abuja ranar Talata, Buhari ya kare manufar sake fasalin naira da Emefiele ya aiwatar, inda ya tabbatar da cewa ta taimaka wajen samar da ingantaccen zabe a 2023.
Tsohon shugaban kasar ya ci gaba da cewa wadanda ke da matsala da manufar sake fasalin naira mutane ne da ke da kudade masu yawa.
Buhari ya ce, “Ba da gangan muka sauya fasanin naira ba da kuma samun karancin kudade da aka yi domin hukunta ‘yan Nijeriya ba. Dimokuradiyya tana ba mutane damar bayyana ra’ayinsu, kuma ba mu yi kokarin hana su ba. Mutane sun fahimci illar bin ra’ayinsu a zaben, kuma ba mu tilasta musu ba.
“Jihata ta Katsina an samu kyakkyawan tsari. A zaben shugaban kasa, APC ta sha kaye. Amma ta samu nasara a zaben gwamna. Watakila sun yi sakaci ne saboda suna tunanin ita ce jihata, kuma suna tunanin za su yi nasara cikin sauki. Mutane ba sa son a yi sakaci wajen gudanar da zabe domin haka zai sa a sha mamaki.
“Na sami Emefiele a ofis a lokacin da na zo a matsayin shugaban kasa, ban samu wasu kwararan hujjoji a kansa da sa in sallame shi daga matsayinsa na gwamnan CBN.
“Idan ka azabtar da mutum bisa zalunci, ba zai iya mantawa ba har tsawon rayuwarsa, don haka idan za ka hukunta mutum, dole ne ka sami kwararen hujjoji. Kuma ya kamata ka sani cewa ba za ka tabbtar a mukami ba har abada. Dole ne wata rana sai ka bar wannan mukamin da kake.
“Lokacin da aka alakanta shi da neman takaran shugaban kasa a 2023, ban tambaye shi ba, saboda bai fada wa kowa ba cewa yana da muradin zama shugaban kasa. In ba haka ba, da na cire shi tare da yi wa al’umma bayanin dalilin da ya sa.
“Babu shakka manufar sake fasalin naira ta ba mu zabuka mai matukar tsafta. Mutanen da ke da makudan kudade ne suka sami matsala da tsarin,” in ji Buhari.