ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ziyarar Ministan Wajen Sin A Afirka: Zumunci Mai Dadi Ba Irin Na ’Yan Ta-more Ba

by Abdulrazaq Yahuza
2 years ago
Afirka

Ziyarar ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, a wasu kasashen Afirka a farkon 2024 kusan al’ada ce da ministocin harkokin wajen kasar kan yi a farkon kowace shekara cikin shekaru 34 a jere.

Irin wannan ziyara da kasar Sin ke yi a farkon shekara tun daga 1991 ta haifar da da mai ido ga Afirka idan aka yi la’akari da yadda aka raya zumuncin aiki da cin gajiyar juna tare da fuskantar kalubalen siyasar duniya domin a gudu tare a tsira tare.

  • Nijeriya Na Fatan Samun Karin Masu Zuba Jari A Taron Kasuwanci Na Duniya
  • Matsafa Sun Sare Kan Budurwa A Adamawa

Duk dan Afirka da ya samu wayewar zamani, har yau mulkin mallakar da Turawan yamma suka yi wa Afirka yana masa daci a rai saboda bautarwa da azabtarwa da kakanninmu suka sha a hannunsu. Wannan ya sa duk lokacin da na yi la’akari da huldar kasuwancin da ke tsakanin Afirka da Sin da sauran harkoki sai na kara fahimtar hujjojin kasashenmu na rungumar Sin.

ADVERTISEMENT

Ziyarar minista Wang Yi, ta karfafa neman goyon bayan Afirka a kan kudurin Sin na kawo ci gaba ga juna a duniya, da tabbatar da ’yanci da tsaro da kuma wayewar kai ta bai-daya da za ta kawo alheri ga kowa da kowa. Irin yanayin da duniya ke ciki yanzu hatta jaririn da ba a haifa ba ya san akwai matsala saboda rashin mutunta hakkin bil’adama da yaudara da rashin mutunta kasashe masu tasowa daga Turawan yamma masu da’awar jagorancin duniya. Abin da Isra’ila ke yi bisa goyon bayan Amurka a yankin Gaza ya nuna hakan baro-baro a fili.

Don haka, Afirka ta yi ma kanta kiyamullaili ta rungumi hulda da Sin domin samun ci gaba. Abin jinjina ne yadda kasashen Afirka 52 suka rattaba hannu a kan yarjeniyoyin tsarin Ziri Daya da Hanya Daya na biliyoyin daloli don samar wa kansu da ababen more rayuwa kamar titunan mota, layukan jirgin kasa, tashoshin teku da sauran abubuwan da ake bukata na bunkasa tattalin arzikin.

LABARAI MASU NASABA

Sin: Ya Kamata Tarayyar Turai Ta Dubi Huldar Tattalin Arziki Da Ciniki Tsakaninta Da Sin Bisa Daidaito

An Gudanar Da Taron “Tattaunawar Magadan Garuruwa Na Duniya Na 2026” A Birnin Beijing

A lokacin da minista Wang Yi ya isa kasar Masar, ya nuna cewa kasar Sin tana goyon bayan adalci ga kowa a duniya musamman kan yakin zirin Gaza wanda ya fara fantsama tare da kai hari a kan jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya.

A tattaunawarsa da shugaban Tunisiya Kais Saied, Wang Yi ya bayyana yadda kyakkawar alaka ta dore a tsakanin kasashen biyu na tsawon shekara 60 tare da jaddada ci gaba da kawance ta fannonin raya kasa da bunkasar tattalin arziki. Shugaban Tunisiya a nasa bangaren ya jaddada goyon kasar Sin a matsayin kasa daya dunkulalliya tare da yabawa da irin nasarorin da take samu ta fuskar ci gaban zamani.

A kasar Togo, minista Wang Yi ya samu kyakkyawar tarba daga takwaransa na kasar, Robert Dussey inda kasar ta Togo ta sake nanata goyon baya ga Sin musamman kan ci gaba da zaman yankin Taiwan a cikinta. Tana mai cewa kasar Sin kwaya daya ce kwallin kwal a duniya.

A kasar Cote d’Ivoire kuwa inda minista Wang Yi ya yada zango na karshe a ziyarar tasa, ya samu tabbaci daga shugaban kasar, Alassane Ouattara cewa ya yi, kasarsa ba ta da babbar kawa ta cinikayya da zuba jari kamar Sin, don haka za ta ci gaba da kyautata zumuncin da ke tsakaninsu. Abin alfahari ba ga Cote d’Ivoire ba kawai har da sauran kasashen Afirka, minista Wang ya ce Sin za ta ci gaba da inganta tsarin cin moriyar juna da Afirka da kuma taimakon kasashen yankin wajen aiki da tsare-tsare mafi kyau da suka fi dacewa da su ta yadda za su ci gajiyar albarkatun da suke da su yadda ya kamata.

Wannan ziyara da minista Wang Yi ya kawo Afirka, ta sake bai wa yankin damar ci gaba da kulla alakar cinikayya mai gwabi a tsakaninsu. Yana da matukar karfafa gwiwa ga kasashen Afirka bisa yadda Sin take samun bunkasar tattalin arziki. Alkaluman da aka fitar na shekarar 2023 sun nuna hada-hadar tattalin arzikinta sun haura fiye da Yuan tiriliyan 126, da ke nufin ta samu ci gaba da kashi 5.2 cikin dari a kan wanda ta samu a shekarar 2022.

Irin wannan ziyara ta ministan wajen Sin, za ta kara bude hanyoyin da Afirka za ta bi sawun Sin ta fannin kere-kere da kirkire-kirkire da zamanantar da kasashensu.

A wata ziyara da na kai shalkwatar Kamfanin China Harbour Engineering Company da ke Nijeriya a Unguwar Maitama, Abuja a wannan Alhamis din, Manajan Daraktan Kamfanin a Nijeriya, Mista Jason Wang ya bayyana min yadda suka kammala aikin titin Keffi (a Jihar Nasarawa) zuwa Makurdi (a Jihar Benue) da kuma kokarin da suke yi na karasa kashi na biyu na aikin wanda zai hade Makurdi da Enugu. Haka nan mun yi magana a kan tashar tekun da kamfaninsu ya samar a Legas ta Lekki wacce za ta samar da dubban aikin yi da biliyoyin kudin shiga ga Nijeriya.

Duk irin wadannan kyawawan abubuwa sun faru ne sakamakon martaba juna a tsakanin Sin da Afirka, ba kamar Turawan yamma da suka zama ’yan ta-more ba.

Afirka
Abdulrazaq Yahuza
+ postsBio
  • Abdulrazaq Yahuza
    https://hausa.leadership.ng/author/abdulrazaq-yahuza/
    Halaye 8 Na Rayuwa Da Aka Fi So A Yi Shiru Maimakon Magana (2)
  • Abdulrazaq Yahuza
    https://hausa.leadership.ng/author/abdulrazaq-yahuza/
    Halaye 8 Na Rayuwa Da Aka Fi So A Yi Shiru Maimakon Magana A Ciki 
  • Abdulrazaq Yahuza
    https://hausa.leadership.ng/author/abdulrazaq-yahuza/
    Saudiyya Ta Taya Nijeriya Murnar Cika Shekaru 64 Da Samun ‘Yancin Kai
  • Abdulrazaq Yahuza
    https://hausa.leadership.ng/author/abdulrazaq-yahuza/
    Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Wata Sabuwar Yarjejeniya Domin Inganta Tsarin Shugabancin Duniya

MASU ALAKA

Sin: Ya Kamata Tarayyar Turai Ta Dubi Huldar Tattalin Arziki Da Ciniki Tsakaninta Da Sin Bisa Daidaito
Daga Birnin Sin

Sin: Ya Kamata Tarayyar Turai Ta Dubi Huldar Tattalin Arziki Da Ciniki Tsakaninta Da Sin Bisa Daidaito

June 4, 2026
An Gudanar Da Taron “Tattaunawar Magadan Garuruwa Na Duniya Na 2026” A Birnin Beijing
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Taron “Tattaunawar Magadan Garuruwa Na Duniya Na 2026” A Birnin Beijing

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo
Daga Birnin Sin

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Next Post
Xi Jinping Ya Bada Muhimmin Umarni A Wajen Bikin Bayar Da Lambar Yabo Ta Injiniya Ta Kasa

Xi Jinping Ya Bada Muhimmin Umarni A Wajen Bikin Bayar Da Lambar Yabo Ta Injiniya Ta Kasa

LABARAI MASU NASABA

Sin: Ya Kamata Tarayyar Turai Ta Dubi Huldar Tattalin Arziki Da Ciniki Tsakaninta Da Sin Bisa Daidaito

Sin: Ya Kamata Tarayyar Turai Ta Dubi Huldar Tattalin Arziki Da Ciniki Tsakaninta Da Sin Bisa Daidaito

June 4, 2026
Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

Arsenal Na Dab Da Ɗaukar Jeremy Monga Daga Leicester City

June 4, 2026
An Gudanar Da Taron “Tattaunawar Magadan Garuruwa Na Duniya Na 2026” A Birnin Beijing

An Gudanar Da Taron “Tattaunawar Magadan Garuruwa Na Duniya Na 2026” A Birnin Beijing

June 4, 2026
Atiku Ne Ya Fi Dacewa Da Tikitin Takara A ADC Amma Ya Kamata Ya Janye — Baba-Ahmed

2027: Kasancewa Ɗan Arewa Kaɗai Ba Zai Tabbatar Da Samun Ƙuri’u Ba – Baba-Ahmed

June 4, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.