Sau da yawa idan jam’iyyar da ke kammala mulki a wa’adinta na biyu kuma tana cikin takarar zaben Shugaban kasa, hankalin wasu mutane ya fi tashi, ganin cewa ko za su rasa wani tagomashin da suke samu daga kasancewar ita gwamnatinidan bata kai labara ba.
Akwai fadin gaba,saboda rudar wasu ne daga cikin Talakawa wadanda ake nuna masu cewa me yiyuwa su shiga cikin halin tagaiyara in suka zabi wata jam’iyya daban,idan sabuwar gwamnati ta hau musamman ma idan ta adawa ce.
- Da Dumi-Duminsa: Buhari Ya Tsige Fadah A Matsayin Darakta Janar Na NYSC
- 2023: Gudummawar Da Ya kamata Jami’an Tsaro Su Bayar
Ita dai gwamnati wadda take rike da kambun mulki na kasa tun wa’adinta na farko ne take fara yi ma kanta kamfe,na kodai su al’ummar kasar su yanke shawarar sake zabenta, bayan ta kammala wa’adinta na biyu.Halin da kuma ake ciki ke nan yanzu babu kuma damar a mayar da hannun agogo baya. Shugaban kasa ba shi kadai bane da zai yi dukkan ayyukan da za su amfani al’ummar kasa ba.Akwai mataimakinsa, Ministoci, Gwamnoni, ‘Sanatoci, ‘yan majalisun tarayya, na Jihohi, Shugabannin kananan hukumomi,kai har ma da Kansiloli,da sauran wadanda suke rike da mukaman siyasa, kowanne daga cikinsu yana da gudunmawar da zai bada, idan Talakawa suka gamsu kan abubuwan da suka yi, har ya burgesu, suka ji dadi za su sake zabenta.Idan kuma aka samu akasin haka to kowa fa sai ya san inda dare yayi ma shi ke nan.Domin kuwa Hausawa sun ce “Ba a fafe gora ranar Tafiya”.Bakin alkalami idan ya bushe ai shikenan.Nagartar abin sayarwar da aka kai kasuwa ita ce zata sa mutane suyi ta rubibin son sayen shi.
Wannan ya na nuna ke nan abu ya zo inji mai tsoron wanka.ita kasar Nijeriya maganar wani sashe ko bangare na kasa yace yana goyon bayan dan takarar daya fito daga sashen,ba wannan lokacin bane aka fara yin shi ba, wani dadadden al’amari ne.
Babu wani sashe na Nijeriya da zai bugi kirji har yace al’ummar bangaren shi ne, ko su kawai sun isa su share ma shi hawaye,har kuri’arsu ta kai shi ga samun nasarar zaben a lokacin.
Irin wannan tunanin sam ba zai yiyu ba,kamar dai mutum ya ce zai iya kirga digon ruwa lokacin da ake ruwan sama.
Ana da ‘yantakarar Shugaban kasa 18 a zaben Shugaban kasar da za ayi watan Fabrairu 2023, hudu daga sashen Kudu maso yamma abinda aka fi sani da kabilar Yarabawa, da suka hada da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu APC,Abiola Kolawale PRP,Omoyele Sowore AAC,Olufemi Adenuga BP,Adebayo Adewole SDP Sai kuma Farfesa Christopher I, AP,.Sashen kudu maso gabas da akwai shida da suka hada da Peter Obi LP,Osita Nnadi APP, Chukwudi Umeadi APGA,Deberechukwu Nwanyanwu ZLP,Dumebi Kachikwu ADC,sai kuma Mazi Okwudili na NRM.Daga sashen Arewa kuma akwai Alhaji Atiku Abubakar PDP, Rabi’u Musa Kwankwaso NNPP,Yabagi Sani ADP,Ado Ibrahim Abdulmalik YPP, Mamman Dantalle APD,sai Hamza Almustafa dantakarar jam’iyyar A A.
Kodai ba ace komai ba da ganin ‘yan takarar goma sha takwas da ake dasu, goma shabiyu daga sashen kudu suke, inda abin ya kasance sashen kudu maso gabas na da shida na Kudu maso yamma kuma na da shida.Kamar yadda abin yake sashen Arewa gaba daya nada shida ko dai ba ace komai ba, sashen Kudu ko nace al’ummar can,ko shugabannin siyasarsu suna da kwadayin mulki ya koma wancan sashen.
Sai dai idan aka yi ma shi al’amarin tunani mai zurfi daga cikinsu ana iya zabo ‘yantakara mutum hudu wato Alhaji Atiku Abubakar,Bola Ahmed Tinibu, Rabi’u Musa Kwankwaso,da kuma Peter Obi.Daga cikin wadannan watakila tun a zagaye na farko cikin ikon Allah ana iya samun wanda yayi nasara,ko kuma sai an tafi zagaye na biyu, koma dai minene daga cikin su wadannan ‘yan takarar da akwai wadanda suna iya kasancewa tamkar ‘yan rakiya ne.Babu wanda ya san abin da yake cikin zuciyar su ‘yantakarar domin wasu ma na iya cewa, magoya bayansu,su jefa ma wani daga cikin su gogaggun ‘yantakarar.
Wannan siyasar da ake ciki ko zabe na gaba wanda ke zuwa ba kasafai bane ake samun ‘yantakara ba, daga sashen Kudu da suka kai har goma sha biyu ba,duk da yake dai na yi magana kan abinda ya sa al’amarin ya kasance haka.
Kowanne bangare yana dogara ne da wani bangare na dan’uwansa domin ya inganta, haka ne al’amarin yake tafiya, shi ne yana samun taimako,manufa anan ita ce babu sashen da za ace shi kadai zai iya kai bante,amma idan ya samu hadin kan wani sashen ko wasu sassan shi ke nan bai da wata matsala.
Haka shi al’amari yake yawan mutane su ne kasuwa ba maganar tarin runfuna ba, kamar yadda marigayi Alhaji Mamman Shata ya bayyana cikin wakarsa mai suna “Isiyaku ka dawo Lafiya, ashe mutane sune kasuwa mu a raba mu da tarin runfuna,”har ma yana karawa da Ye yeyeye yeyyere, ye dan turmi sha daka, ye dutse sai mirgina”. Maganar gaskiya kuma haka ne shi al’amarin yake domin an gina kasuwa mai yawan runfuna ya kuma kasance babu mutane, ai tamkar an gudu ba a tsira ba ke nan.
Kamar idan aka dubi shi yankin ko sashen Kudancin Nijeriya akwai marigayi Dakta Nmandi Azikwe,Janar Aguiyi Ironsi Janar ritaya Aremu Olusegun Obasanjo, Earnest Shonekan, Goodluck Ebele Jonathan.Yayin da shi kuma sashen Arewacin Nijeriya akwai marigayi Sir AbubakarTafawa Balewa,ritaya Janar Yakubu Gowon,marigayi Murtala Ramat Muhammed,ritaya,marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, ritaya Janar Muhammadu Buhari, ritaya Ibrahim Badamasi Babangida,ritaya Janar Abdulsalam Abubakar,marigayi Janar Sani Abacha,da kuma marigayi Umar Musa ‘Yar’adua.
Koma ba a ce komai ba shi sashen Arewa yafi yawan wadanda suka Shugabanci ita kasar Nijeriya inda yake da tara,sashen Kudu yana da biyar,ko ba a ce komai ba sai an fadawa mutum wadanda suka fito daga sashen ne suka dade suna Shugabanci.
Shi kuma sashen Kudanci biyar ne da aka yi mata fifiko da hudu, amma idan ana maganar cigaba tsakanin da ita Arewa “Koda girgiza Hausawa sun ce Kanya tafi Magarya ‘ya’ya”wannan magana haka take babu ja tunda Kare ya mutu a saura (wurin da aka dan dade ba a noma shi).
‘Yan siyasa na kowanne sashe sune suka fi sanin hanyoyin da za su bi na bullo ma shi al’amarin yadda hakan zai kai su ga samun nasara,sai dai wani abu kada a saki reshe a kama ganye.Masu zabe sune yakamata ‘yantakara su rika zawarcinsu.
Wani abu da yake da daukar hankali shi ne yadda ‘yan kabilar Ibo na sashen Kudu maso gabashin Nijeriya,da basu damu da maganar yin zabe ba, amma sai ya kasance wannan lokacin suna yin gaba- gaba wajen maganar rajistar yin zabe.Bugu da kari yanzu akwai majami’un da basu barin wani ya shiga sai ya nuna shedar katin zaben shi. kafin a kai ga barin shi ya shiga.
Ita ma kungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere ta sauya kudurin data fara furtawa na goyon bayan dantakarar LP Peter Obi, tace saboda gaskiya da dalci kamata yayi dan kabilar Ibo shi zasu goya ma baya.Yanzu abin ya dawo ‘yar-gida saboda kuwa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC suke goyan baya.
Shi kuma sashen na Arewa Shugabannin Dattawan Arewasu suka gana da ‘yan takara da suke ‘yan gaba- gaba na jam’iyyun APC, PDP, NNPP, da kuma LP,sai dai basu yanke shawara ba kan wanene suka ya dace a zabe. Koma za suyi hakan watakila sai nan gaba, to Budurwa dai tamkar wata haja ce kowanne kuma da tayin da yake mata amma mai sayen ta daya ne.Nijeriya Allura ce cikin ruwa mai rabo shi ka dauka, a kuma tuna Allah shi ne ke bada mulki ga wanda ya so.