Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wani sakon taya murna ga bikin baje kolin sana’o’i masu alaka da fasahohin zamani na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2023 a kwanan baya, wanda ya janyo yabo daga al’ummun sassa daban daban, inda aka bayyana cewa, sakon shugaba Xi ya nuna muhimmancin raya sana’o’i, da tattalin arziki masu alaka da fasahohin zamani, gami da hanyar da za a bi wajen inganta wannan fannin, ta yadda za a samu damar karfafa hadin gwiwar da kasar Sin take yi tare da sauran kasashe, ta fuskar fasahohi na zamani.
A cikin sakon shugaba Xi, akwai wata jimlar da ta janyo amincewa sosai daga kasashe daban daban, wadanda suka halarci bikin baje kolin sana’o’i masu alaka da fasahohin zamani na wannan karo, wadda ita ce “gaggauta kafa wata al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a fannin yanar gizo ta Internet, don neman tabbatar da makoma mai haske”.
A nasa bangare, minista mai kula da kimiyya da fasaha na kasar Argentina, Daniel Filmus, ya ce, dukkan kasashe dake yankin Latin Amurka, da na Caribbean, suna son hadin kai tare da kasar Sin, ta yadda za su samu damar raya tattalin arzikin kansu.
Yanzu haka kasar Argentina na kokarin samar da jerin manufofi na inganta bangaren kimiyya da fasaha na kasar, gami da neman damar hadin gwiwa tare da kasar Sin da sauran kasashe, da zummar raya bangarorin aikin gona, da na lafiya, da ilimi, da masana’antu na kasar, da fasahohi na zamani. (Bello Wang)