Dan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2023 a Jihar Kano, Murtala Sule Garo, ya yi wa al’ummar Musulmi barka da sallah tare da bukatar Musulmi su dage wajen yi wa kasar nan addu’a.
Wannan na cikin wani sakon taya murnar sallah karama, inda ya ce bikin sallar bai takaita ga kammala azumin wajibi na watan Ramadan ba.
- Gidauniyar Saraki Ta Kammala Shirin Rabon Abincin Buda-baki
- Sallah Ƙarama: Abun Da Ya Kamata Ku Sani Kan Sallar Idi Da Ladubanta
Ya ce sallah na da nufin fadakarwa da tunatarwa a tsakanin al’umma don ganin an samu zaman lafiya da arziki mai dorewa a Jihar Kano da ma Nijeriya baki daya.
“Ina taya al’ummar Musulmi musamman na Jihar Kano murnar barka da sallah.
“Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya ba mu ikon azumtar watan Ramadan. Allah Ya karbi ibadunmu, ya yafe mana kurakuranmu, ya kuma kara ara mana lokaci nan gaba.
“Ina kira ga Musulmi da su yi amfani da darusan da muka koya cikin wannan wata mai alfarma don tabbatar da zama lafiya da kaunar juna a jiharmu da ma kasa baki daya.”
Har wa yau, ya ce tabbas ‘yan Nijeriya na fuskantar matsin rayuwa sakamakon tabarbarewar tattalin arziki, amma ya ce kada a cire tsammani.
“Tabbas ‘yan Nijeriya na cikin wani mawuyacin hali sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin da ake fuskanta.
“Amma duk da haka ba mu cire kauna ga kasarmu ba. Don haka wannan lokaci ne da za mu ci gaba da addu’o’i domin Allah Ya kawo mana mafita.”
Garo ya yi fatan Musulmi za su yi bukukuwan sallah karama cikin koshin lafiya da wanzuwar zaman lafiya.