Sanata Aliyu Wamakko ya tabbatar da sakin fursunoni 62 da ake tsare da su a gidajen yari daban-daban da ke Jihar Sakkwato.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bashar Abubakar, mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai na Wamakko ya fitar ranar Alhamis a Sakkwato.
- Karamar Sallah: Buhari, Tinubu, Atiku, Lawan, Gbajabiamila Sun Bukaci Zaman Lafiya
- Masar Dankali Ta Musamman Don Bikin Sallah
Fursunonin sun kasance a gidajen gyaran hali na Sakkwato, Tambuwal, Wurno da Gwadabawa.
Sanatan ya warware tarar da kotuna suka yi wa fursunonin domin a sake su.
Wammako mai wakiltar Sakkwato ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya kuma bai wa kowane daga cikin fursunoni 62 da aka sako Naira 10,000 domin su kai kansu gida.
Ya ce sun yi hakan ne domin a basu damar gudanar da bukukuwan Sallah tare da iyalansu.
Sanatan ya shawarce su da su kasance masu halin kirki, su guji maimaita kura-kurai da suka kai su wuraren gyara.
Wadanda suka ci gajiyar shirin sun yaba wa Wamakko bisa wannan gagarumin karimcin tare da yin alkawarin za su kasance da kyawawan halaye yayin da suke komawa ga al’umma.
Kamfanin dillancin labarai (NAN) ya rawaito cewa dan majalisar ya kaddamar da shirin ne a shekarar 2016, a wani bangare na shirinsa na taimakon jin kai.