• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Salman Rushdie: Wanda Ya Yi Batanci Ga Annabi Na Cikin Mawuyacin Hali Bayan Kai Masa Hari

by Sadiq
3 years ago
Salman Rushdie

Salman Rushdie na cikin mawuyacin hali game da rayuwarsa bayan kai masa hari da aka yi, wanda ya shafe tsawon shekaru yana buya sakamakon batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

An kai wa fitaccen marubucin hari, wanda aka kwashe shekaru da dama ana yi wa barazanar kisa bayan ya rubuta littafin The Satanic Verses.

  • Daga Asabar 8 Zuwa Talata 11 Ga Watan Muharram 1444
  • Yunkurin Amurka Kan Sana’ar Kera Sassan Na’urorin Laturoni Ba Zai Yi Nasara Ba

Jaridar New York Times ta ruwaito cewa an kai masa harin ne safiyar ranar Juma’ar yayin da yake jawabi a wurin wani taro a Yammacin Jihar New York da ke Amurka.

Marubucin, wanda ya lashe kyautar The Booker Prize, yana jawabi ne a Cibiyar Chautauqua yayin da aka kai masa hari.

Ganau sun ce sun ga wani mutum ya ruga a guje ya hau kan dandamalin da marubucin yake jawabi, inda ya rika naushi yana kuma daba wa Mista Rushdie wuka a yayin da ake gabatar da shi gaban jama’a.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan intanet ya nuna mahalarta taron sun ruga a guje kan dandamalin don kai masa dauki.

Bayanai sun nuna cewa akwai alamun an daba masa wuka a wuya, wanda ya zuwa yanzu yake cikin mawuyacin hali.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito ’yan sanda na cewa an daba wa wani mutum wuka amma sun ki cewa komai game da ko wane ne.

Marubucin wanda dan asalin India ne, ya shahara ne bayan ya rubuta littafi mai suna Midnight’s Children a shekarar 1981, wanda aka sayar da kwafi fiye da miliyan a Birtaniya kadai.

Sai dai littafi na hudu da Mista Rushdie ya rubuta a 1988 – The Satanic Verses – ya tilasta masa shiga buya tsawon shekaru tara.

Littafin ya gamu da fushin Musulmai, wadanda ke ganinsa a matsayin batanci ga addini, inda aka haramta sayar da shi a wasu kasashe.

An ruwaito cewa, shekara daya bayan wallafa littafin, Shugaban Addinin Iran, Ayatollah Khomeini ya sanya ladan Dala miliyan 3 ($3m) ga duk wanda ya kashe Mista Rushdie.

Mutane da dama ne suka mutu sakamakon tarzomar da ta barke kan wallafa littafin, ciki har da wasu da suka fassara littafin zuwa wasu harsunan.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum
Manyan Labarai

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”
Labarai

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Next Post
2023: Ko Yawan Masu Rajistar Zabe Zai Iya Tasiri Ga ‘Yan Takara?

2023: Ko Yawan Masu Rajistar Zabe Zai Iya Tasiri Ga ‘Yan Takara?

LABARAI MASU NASABA

Salman Rushdie

Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa

October 27, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Hatsarin Jiragen Ruwa

Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe

October 27, 2025
Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.