Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MANYAN LABARAI

Sam Nda-Isaiah: Ba Rabo Da Gwani Ba

by Muhammad
December 16, 2020
in MANYAN LABARAI
4 min read
Rabo Da Gwani
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Sharfaddeen Sidi Umar,

Shakka babu rasuwar Kakaki Nupe, Shugaban Rukunin Kamfanin LEADERSHIP, Mista Sam Ndanusa Isaiah, babban rashi ne maras misaltuwa, wanda ya shiga cikin kundin tarihin da Nijeriya da al’ummarta ba za su taba mantawa ba a nan kusa ko can gaba ba saboda dalilai da dama.

samndaads

Tabbas hakika ga duk wadanda suka san Ciyaman da ayyukansa kai tsaye za su bayyana ranar Juma’ar da ya koma ga mahalliccinsa a matsayin bakar bahaguwar rana da ta katse numfashin jajirtaccen mutum mai kishin kasa da son ci-gaban ta.

Rasuwarsa ta haifar da jimami, alhini, firgici, zulumi da bakin ciki maras iyaka ba ga iyalai da ‘yan uwansa kawai ko ire-ire na da ke aiki a karkashinsa ba, a’a, rashi ne da ya shafi dimbin jama’a wanda babban rashi ne ga al’ummar kasar da ke burin ganin an samu sauyi da canji mai ma’ana kan yadda ake shugabantar al’umma a farfajiyar siyasar Nijeriya.

A yau Arewa da al’ummarta wadanda ke cikin gararin matsalolin tsaro da koma baya sun yi rashin dan kasa nagari mai tsananin kishin Arewa da muradin ganin yankinsa ya yi wa tsara fintinkau a fagen siyasa, shugabanci, aikin Gwamnati, kasuwanci, aikin gona, masana’antu da sauransu da dama.

Ciyaman ya samarwa kansa suna wajen fashin bakin lamurran yau da kullum, iyo da ninkaya a kogin matsalolin al’umma da hanyoyin magance su. Makaranta kan nazarcin shafinsa ‘Last Word’ (Babbar Magana) a kowacce Litinin (a Turanci) da Juma’a (a Hausa), domin marubuci ne wanda ya cancanci samun dukkanin karramawar da a ke yi wa hazikan, jajirtattun ‘yan jarida kuma marubuta masu kishin kasa da kokarin bunkasa Harshen Hausa da Hausawa.

Ba ciri ba coge! A duniyar tarihi Ciyaman yana sahun farko na wadanda ke azamar raya Harshen da ba nasa ba wanda kuma ya dauka a matsayin harshensa na biyu. Fara wallafa LEADERSHIP Hausa a ranar 22 ga Satumba 2006 a mako-mako wadda ta fara zama jaridar Hausa da ta fara fita kullum a 2017 da canjin suna zuwa LEADERSHIP A YAU ya tabbatar da hakan.

Kakaki Nupe mutum ne mai son ganin matasa sun zamo masu dogaro da kai ta hanyar taimakon kansu da na kasa da su wanda a kan hakan ne ya baiwa matasa da daman gaske damar aiki a karkashinsa a LEADERSHIP da sauran fannoni da dama na kamfunansa a ciki da wajen kasar nan.

Kasancewar Ina cikin sahun farko na makarantan LEADERSHIP tun farkon kafuwarta  a 2004 shekaru da dama kafin fara wallafa LEADERSHIP Hausa, wadda na zama wakilinta na Jihar Sakkwato shekaru 12 zuwa yau, na san kima, tasiri da daukakar alkalamin Ciyaman da muhimmiyar rawar da yake takawa.

A bayyane yake cewar tsinin alkalamin Ciyaman ba ya razana, shakku, tsoro, ko fargaba, ballantana kunyar idanun kowa a duniya. Hasalima a duniyar zamaninsa ‘yan jarida da marubuta sun dauke shi a matsayin abin koyi da kwatance.

Ga dukkanin wadanda ke biye da rubuce-rubucensa a jaridun Trust har zuwa LEADERSHIP za a san lallai Ciyaman ya san Nijeriya wadda ke a tafin hannunsa, ya kuma san mene ne shugabancin al’umma wanda a kodayaushe yake bayar da shawarwari da hanyoyin gyara a aikace.

Mawallafin LEADERSHIP mutum ne wanda a kowane hali, a kowane irin yanayi, a kuma ko wane irin lokaci, burinsa, fatarsa da hangensa shine ya ya za a yi ya taimaki al’ummarsa, tunaninsa shine ta yaya zai fito da abubuwan da za su kawo ci-gaban al’umma, hangensa shine wace gudunmuwa zai bayar domin kawo gyara ga inda ke bukatar gyara, da canji ga inda ke bukatar canji.

Alkiblarsa a dare da rana ita ce wace hanya za a bi domin ceto Nijeriya da al’ummarta daga fadawa mummunan ramin da Gwamnatoci da gurbataccin shugabanni ke dora ta a kai. Yadda ya fito a fili ya yaki tazarcen da Obasanjo ya so ya nema a karo na uku babban misali ne na zamansa jajirtaccen dan kasa da ya tsayu haikan domin ganin ba a yi wa tsarin mulkin kasa katsalandan ba.

Shakka babu Ciyaman ya yi bankwana da duniya a yau, amma halayensa nagari da kyawawan ayyukansa za su ci-gaba da bibiyarsa kamar yadda kuma tarihi da mabiya tarihi za su ci-gaba da tunawa da shi tare da adana shi a cikin kundin musamman na wanda ya bayar da gagarumar gudunmuwa ga ci-gaban kasa, bunkasa aikin jarida, hobbasar wanzar da shugabancin gaskiya da adalci, yunkurin tabbatar da siyasa tagari da samarwa al’umma kyakkyawar makoma.

A yanzu haka dai a na nan a na cigaba da yin tururuwar zuwa ta’aziyyar wannan mashahurin jarumi kuma gwarzo dan gwagwarmaya daga sassa daban-daban na Nijeriya da ma duniya bakidaya.

 

Sidi Umar shi ne Wakilin LEADERSHIP A YAU A Sakkwato.

SendShareTweetShare
Previous Post

Tun Farko Sarki Sanusi Bai Cancanci Zama Sarkin Kano Ba, Inji Ganduje

Next Post

A Karshen Disamba Za A Kulle Duk Layin Wayar Da Ba A Yi Rajistarsa Da Katin Dan Kasa Ba – NCC

RelatedPosts

Bude Makarantu

Korona: Ba Ja Baya Ga Bude Makarantu – Gwamnatin Bauchi

by Muhammad
6 days ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi ta...

Harshen Hausa

Taron ‘Waiwaye Adon Tafiya’: Masana Sun Damu Bisa Nakasta Harshen Hausa

by Muhammad
7 days ago
0

Akwai Damuwa Kan Yadda Zamani Ke Tafiya Da Al’adun Bahaushe...

'Yan Kwaya

Zaben Kananan Hukumomin Kano: Yadda Aka Tono ’Yan Kwaya A ’Yan Takara

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta...

Next Post
A Karshen Disamba Za A Kulle Duk Layin Wayar Da Ba A Yi Rajistarsa Da Katin Dan Kasa Ba – NCC

A Karshen Disamba Za A Kulle Duk Layin Wayar Da Ba A Yi Rajistarsa Da Katin Dan Kasa Ba - NCC

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version