Ahmed Muhammed Danasabe" />

Sam Ndah-Isaiah: Tun Farkon Haduwa Da Shi Na San Mutumin Kirki Ne

Sam Ndah-Isaiah

Na fara haduwa da Marigayi Sam Nda  Isaiah a garin Lokoja NE a 2010 lokacin Ina yin aiki da rusasshiyar jaridar “The Republic” a matsayin wakilinta a jihar Kogi.

Ina daga cikin ‘yan jaridun da su ka  yi hira da marigayin a waccan shekara ta 2010,

lokacin  da ya kawo ziyara jihar Kogi don halartan bikin ranan Bassan-Nge (Basan-Nge Day) wanda al’ummar ta Bassan-Nge suke gudanarwa a ranan 26 ga watan Disamban kowace shekara.

Akwai tambayar da na yi ma sa bayan mun kammalla hira da shi, inda na kebe shi  na tambaye shi cewa, “Shin ranka ya dade, gaskiya kai  dan asalin jihar Kogi ne? Sai marigayi Sam Nda Isaiah ya dube ni yayi murmushi.

Zuwa can sai ya kada baki ya ce mini “Ai jihohin Kogi da Neja, Danjuma ne da Danjummai” haka ma “Al’ummar Nupawa da Bassan-Nge”.

Daga nan, muka ka yi ban kwana da juna, kuma karshen gani na da shi kenan, har sai dana samu labarin rasuwarsa a ranan Juma’a 11 ga watan Disambar 2020.

Amma ina ganinsa, na san yana da kirki.

Duniya ta yi rashin gawurtacce kuma gogaggen dan Jarida wanda samun cike gurbinsa zai yi wuya.

Ba zan taba mantawa da marigayin ba domin kuwa ta dalilinsa ne ya sa na sake yin fice  a matsayina na dan jarida a jihar Kogi, musamman a tsakanin Hausawa da Nupawa wadanda ba su da wata jarida da suka dogara da ita kuma suke rubibun saya a kulli yau min sai jaridar Leadership A yau wanda marigayi Sam Nda Isaiah ya kafa.

Daidai gwargwado, marigayi Sam Nda Isaiah ya bada gudunmawrsa wajen ci gaban Nijeriya ta fannin siyasa da kuma tattalin arziki.

Addu’a ta gare shi, ita ce Allah ya jikansa da rahama. Ya baiwa iyalansa da yan uwa da abokan huldarsa da kuma daukacin ma’aikatan jaridar Leadership hakurin jure wannan babban rashin da suka yi.

 

Dan Asabe shi ne Wakilin LEADERSHIP A YAU a Jihar Kogi.

Exit mobile version