El-Zaharadeen Umar" />

Sana’ar MC: Dole Sai Ka Na da Ilimin Abin, Inji MC Bahaushe Katsina

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Sana’ar san kira, da aka sani a zamanin da, wanda yanzu aka zamanantar da ita, ta koma MC ta zama wata babar madogara ga wadanda suke yin ta domin samun kudaden shiga, sannan ta zama sai wanda Allah Ya huwacewa iya magana yake iya tasiri wajen yin ta.

Wannan sana’a ta kara fito da martabar masu yin ta tun daga lokacin da ‘yan zamani wato ‘yan Boko suka shiga cikinta tsundun, ganin yadda aka fara yin watsi da ita da kuma raina wanda yake gudanar da ita saboda kallon da ake yi mata tun asali.

Bayan haka yanzu matasa masu jini a jika ne suka mamaye kafatalin wannan sana’a ta MC musamman a arewacin Najeriya kuma sana’a ce da aka bayyana cewa tana kawo rufin asiri, da kara gogewar magana agaban dubun dubatar jama’a.

MC BAHAUSHE matashi ne da yake da nasibi da sa’ar rayuwa, ya kuma zama abin kwatance a cikin wannan sana’a ta MC ya kuma zagaya jahohi da dama domin gabatar da wannan sana’a yana daga cikin wadanda suka zama sha kuru kudum kuma jigo domin tabbatar da nasarar taro ko biki ko kuma suna, inda ake yi masa kirara da cewa duk bikin da Bahaushe bai je anyi bikin ba tsari.

To wai wane ne MC Bahaushe? mai ya kai shi shiga wannan sana’a da ake yi wa kallon kaskanci, wace irin riba ya ci a cikinta, menene madogararsa? wace irin nasara ya samu? kai menene tarihin rayuwarsa da kuma karatunsa?

A cikin wannan tattaunawa da ya yi da LEADERSHIP A Yau a Katsina ya fede biri har wutsiya, sannan ya yi manuniya da yadda ya kamata a rika gudanar da wannan sana’a ta su ga wadanda suke sabon shigar wannan sana’a ta MC ya kuma bayyana dalilinsa na shiga wannan sana’a.

Mene ne sunanka da tarihin rayuwarka da kuma karatunka?

Suna na Kwamared Kabir Sa’idu Bahaushe Dandagoro ana kira na da MC Bahaushe. Ni dan Dandagoro ne a karamar hukumar Batagarawa, na yi firamare da Sakandare na duk a Batagarawa sannan na kammala karatuna a Jami’ar Umaru Musa Yar’adua a shekarar 2016. Yanzu haka ina aiki da gidan Rediyon Bision F.M Katsina, sannan na zama mai gabatarwa a wajen tarurruka ‘’San Kira’’ wanda kuma ake kira da turance Corporate Mc.

Yaya kake gudanar da wannan sana’a ta MC a wannan zamani?

To, da yake mutane da yawa ba su da masaniyar cewa jan taro na bukatar kwarewa ta musamman da kuma Ilimi da kuma baiwa. MC na nufin ‘Master of Ceremony’ watau wanda shi ke da ruwa da tsaki dangane da nasara ko akasin haka awajen taron. Mai rike Lasifika ya gabatar da komai na taro, ya ba mai magana ko kuma ya yi jawabin kansa ko hana surutu da zirga-zirgar mutane da ba su dariya da ilimantar da su. Ana yawan yin haka a wajen tarurrukan Kungiyoyi da Siyasa da na Gwamnati da Bukukuwan Suna da Aure da murnar zagayowar ranar haihuwa da na wayar da kan al’umma da dai sauransu da dama.

Ina kokarin gabatarwa ta cike da rike mutane da jawabi da ban dariya tare da gwanintar harshe da bincike na musamman domin canza tsarin da aka saba don tabbatarwa jama’a cewa Sana’a ce mai karfi da bata bukatar jarin kudi sai sutura da kuma magana.

Wadanne Irin nasarori ka samu tun daga fara wannan sana’a zuwa yanzu?

Gaskiya Alhamdulillah, tun a baya da na shiga na fara na samu rufin asiri da kuma kudade tun ina makaranta. Don kana zaune abinka za a zo da biki, ko wani taro a ba ka kudi tun ma kafin lokacin taron ya yi. Bayan kyaututtuka, ina cikin gabatarwa ban roka ba wani ya ba ka waya ko kudi ko kuma ya nuna maka kaunarsa gare ka. Ta yadda duk inda ya ganka sai ya ji dadi ya maka magana ya ce wane ne. Sannan ina da Manajana da yarana da abokai masu shiga hidimata muna tafiya tare kuma duk muna karuwa da juna. Na taba karbar lambar girmamawar Fitaccen mai gabatarwa a shekarar 2016 daga daliban da suka gama Jami’ar Umaru Musa a shekarar 2016. Har ta kai yanzu tun kafin taro da watanni ana nema na a biya ni don in yi, na fita jihohin arewa da dama na yi wannan aikin nawa da sauran manyan wurare a gaban manyan mutane.

Ko kamar taro nawa kayi da kuma shekarun da ka dauka kana MC?

Gaskiya abin da yawa tunda ba tantancewa ake yi ba, sun tasamma 200 kuma na shekara bai fi biyu ba ina yi…

Wane irin kalubalen wannan sana’a ta MC take fuskanta a wannan zamani?

Eh! ba a rasa wa, gaskiya ba na son ina aiki ga shi a rubuce a hannuna wani ya zo wanda ma ba ya cikin taron sosai, ya ce min kaza zan yi, ko kuma mutum ya gayyace ni bai biya ni ba, har ranar taron, don idan ma ban ji kudin hannuna ba to bana zuwa. Sai kuma mawakan da za su zo taro ba a gayyace su ba, su dame ka da ka kirawo su, da kuma wadanda aka gayyata din ace su tsaya amma su ki tsayawa, sai sun ga dama. Da ma kallon da wasu ke yi mana kamar maroka ko kuma ai MC kowa zai iya, sai a rika kiran abokai da ‘Yan uwa suna yi, alhali tun daga tsayuwarsu ma za a ga suna kyarma ko su fadi wani abu duk taron ya watse!

Da ka yi magana maroka menene ya banbanta aikinku da kuma roko a wajen tarurruka?

su koda mutun suke yi suna rokon kudi lokacin gudanar da taro, mu kuma gabatar da taron muke yi ba roko, sannan duk wanda ya zo muna kokarin fadin cewa ya zo, domin hakan na daga cikin ilimin gabatar da taro

Shin ko akwai wani tsayayyan farashin wannan sna’a ta kuma ko kuma ya abin yake?

Alhaji batun farashi kishin Dankali ne, ai ka san Babba ne yake danne karami ko?

Ban sani ba, kila ko wannan sana’a taku tana bukatar wani taimako ko tallafi ko kuma shawara daga jama’a?

To gaskiya duk mai yin wannan sana’ar ba ya bukatar tallafi don mu biyanmu ake yi ba mu kashe ko sisin kwabo ba, sana’a ce marar jari sai magana kawai. Bukatarmu ga jama’a shi ne, su rika baiwa abu hakkinsa a lokacin da ya da ce. Ko gwamnati ta rika sanyawa muna jan tarurrukanta saboda mai laya dole ne ya kiyayar mai zamani. Sannan a rika tsara taro a rubuce kuma a rika fada mana da wur-wuri, a daina yi mana Katsalandan. A rika bambance mu da yan bikin dangi da abokai, mu kwararru ne kuma gogaggu, duk da Alhamdulillah gaskiya muna kara daraja ana mutunta mu a idanun jama’a sosai.

Da ka yi magana kwarewa, ka taba halarta wani taron karawa juna sani akan wannan sana’a taka ta MC?

A’a, sai dai ina bin diddigin litattafan da aka rubuta a yanar gizo domin neman ilimin yadda ake gabatar da taro da kuma magana a bainar jama’a, saboda zai yi wuya ka samu cewa gashi ana taron karawa juna sani, akan harkar gabatarwa, sai dai kawai tarurrukan kungiyoyi da akan yi gwaji.

Idan aka tambayeka shawara wace irin shawara zaka baiwa abokan sana’arka ta MC?

Kwarai kuwa. Kyau ace muna da kungiya ta Kasa da jihohi, sannan kuma yawancinsu ba su baiwa kafafen sadarwar zamani muhimmanci watau soshiyar midiya kamar ni ka ga ina yin Bidiyo na minti daya ina sakawa a shafin ‘Instagram’ dina da hotunan ayyukan da duk nake yi. Kuma ina yin hira da kafafen yada labarai. Sannan kyau a rika karo dubaru ana koyon yadda za a rika canzawa daga yadda ake yin abu ada, don ta internet babu abin da ba za iya koya ba, akwai litattafai da yawa na koyon sana’ar nan mai albarka. Sannan akwai masu yin aikin nan sai su mai da shi kamar Gala suna kira ana ta liki, ko ana biki suna ta tambada mutane, ko kuma ka ga MC amma babu sutura mai kyau.

Daga karshe me kake son zama ta hanyar wannan sana’a ta MC?

ina son in kafa tarihi kamar yadda na fara kafawa a yanzu, ta hanyar bayanin yadda ake gabatar da wannan sana’ar wanda a iya cewa na zama mutun na farko a yankin arewa da aka fara tattaunawa da shi a kafafen yada labarai domin kara sanin mahimmancin wannan babbar sana’a ta MC. Sannan ina son jama’a su fahimce cewa mai gabatarwa ko MC shi ne shugaban taro a wannan lokaci, kuma yana bukatar a fahimci aikinsa ta hanyar bashi goyan baya domin samun nasarar taro. Daga karshen ina yi wa kowa fatan alheri.

Exit mobile version