Sanata mai wakiltar Mazaber Nasarawa ta Kudu, Alhaji Umar Tanko Al-makura ya taimakawa manoma a mazabersa da takin zamani da maganin kwari da kuma maganin kashe ciyawa a gonakai.
Takin zamanin an raba shi zuwa Kananan Hukumomi biyar da Sanatan ke wakilta da suka hada da Lafiya, Doma, Keana, Awe da kuma Obi.
- An Bude Bikin Fina-finai Na Kasa Da Kasa Karo Na 12 Na Birnin Beijing
- Wike Ga Atiku : Kar Ka Zarge Ni In Ka Fadi A Zabe
Sanatan ya ce takin zamanin tirela daya mai dauke da buhu 600 za a tura kowani karamar hukuma.
Ya ce makasudin yin wannan shi ne, saboda Nasarawa ta kudu yanki ne na manoma masu tarin yawa, shi ya sa ya yi amfani da wannan damar ganin yadda takin zamani yake tsada.
Da yake jawabi Mukaddashin Gwamnan Jihar Nasarawa, Dakta Emmanuel Agwadu Akabe ya ce wannan tallafin da sanatan ya yi wa al’umman mazabersa ya cancanta, saboda jama’an mazaber za su amfana.
Ya kuma yi kira ga mutanin da suka samu wannan tallafin da su yi amfani da shi ta hanyoyin da ya dace.