Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, na kokarin dakile yunkurin tashin daya daga cikin manyan kantunan Nijeriya, Shoprite, na rufe reshensa daya tilo da ke jihar Kano.
Kantin Shoprite shahararren kantin sayar da kayayyaki ne da aka sanya wa suna Ado Bayero Mall a cikin birnin Kano, a makon da ya gabata ne Shoprite din ya sanar da matakin da yake shirin daula na ficewa daga cibiyar kasuwanci ta Arewacin Nijeriya a watan Janairun badi, yana mai dora alhakin tashin da kan “kalubalan tattalin arziki.”
- Mukamin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai: Tsakanin Barau Jibrin Da Saura
- Shirin Tinubu Na Samar Da Tabarau Miliyan Biyar Ga Masu Fama Da Ciwon Ido
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, ana ci gaba da samun ra’ayoyi jama’a mabambanta kan matakin da hukumar gudanarwar kantin ke shirin dauka a reshensu na Kano.
Wata sanarwa da mai baiwa Sanata Barau shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a Ismail Mudashir ya fitar a yammacin ranar Litinin, ta ce, mataimakin shugaban majalisar dattawan zai gana da mahukuntan kamfanin a cikin makon nan a Abuja kan lamarin.
“Za mu ga abin da za mu iya yi don karfafa musu guiwa su janye shawarar da suka yanke don su ci gaba da zama a Kano. Kamar yadda kowa ya sani, akwai dimbin damarmakin kasuwanci a Kano, cibiyar kasuwanci ce ta Arewacin Nijeriya,” cewar Mudashir.