Daga Muhammad Maitela,
Shugaban Majalisar Dattawa a tarayyar Nijeriya, Sanata Ahmad Lawan ya ziyarci tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Kwankwaso domin yi ma sa ta’aziyyar mahaifin sa, tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalai da yan uwan Sheik Ahmad Lemu.
Sardaunan Bade, Sanata Lawan ya sanar da hakan a sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun mai taimaka masa a harkokin yada labarai, Alhaji Babangida Inwa Jibrin, ranar Asabar inda ya bayyana cewa a addini da al’adunmu na yan Nijeriya, ba mu da sabani ko bambancin ra’ayi.
Dr. Lawan ya kai ziyarar a birnin Kano tare da shugaban riko na jam’iyyar APC, Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni hadi da rakiyar mataimakin mai tsawatar wa a zauren majalisar dattawan, Sanata Sahabi Yau Kaura.
Bugu da kari kuma, shugaban majalisar tare da Gwamnan Yobe sun gudanar da gaisuwar ta’aziyyar tare da addo’o’i na musamman ga mahaifin Sanata Kwankwaso a gidan sa da ke Miller Road, a Bompai, dake birnin Dabo kana da kai ziyara a kushewar marigayin.
“Wannan rashi ne namu baki daya, saboda a addinance da al’adunmu sun koya mana hadin kai da mutunta juna. Har wala yau, sun koya mana yadda za mu rinka yin tarayya da jama’a murna a duk lokacin da abin farin-ciki ya same su tare da alhinin dangane abin damuwar da ya samu daya daga cikinmu cikin mutunta wa. Wannan shi ne abinda ya dace mu yi.”
“Saboda haka mu na addu’a ga Ubangiji Allah ya jikan baban mu kuma ya yafe masa kurakuransa. Wanda kuma kowa ya shaidi marigayin cikakken dattijo mai kokari tare da hada kan jama’a a cikin kyakkyawar rauwa a fannin sadaukarwa. Baba ya tafi amma ba za mu gushe ba muna kewarsa tare da tunawa da dimbin ayyukan ci gaban jama’a, Allah ya sa aljanna ce makimarsa.” Dr. Ahmad ya nanata.
A nashi bangaren, Sanata Kwankwaso ya bayyana matukar godiya dangane da wannan ziyarar ta’aziyya mai cike da girmama wa gareshi da iyalai da sauran yan uwan su a aka kawo wa ziyarar ta’aziyyar.
A hannu guda kuma Babangida Jibrin ya kara da cewa shugaban majalisar, Dr. Ahmad Lawal, ya mika jajen ta’aziyya ga yan uwa da iyalan babban malamin addinin musulunci, Sheik Ahmed Lemu, wanda Allah ya yi wa rasuwa, wanda ya bayyana rasuwar Shehin malamin a matsayin babban rashi ga al’ummar musulmin Nijeriya da ma duniya baki daya.
“Har wala yau, na yi imani kan cewa dole wannan rashin ya girgiza ku, ganin yadda ku ka rasa uba kuma nagartaccen masanin addinin Musulunci.”
Wanda a karshe shugaban majalisar dattawan ya yi addu’ar samun jinkan Allah ga marigayi Sheikh Ahmed Lemu kana ya bai wa yan uwa da iyalansa hakurin jure rashin.