Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Sanata Abdul Ningi, ya koma majalisa bayan dakatar da shi na tsawon watanni uku.
An dakatar da shi a watan Maris saboda zargin yin cushe a kasafin kudin 2024.
Sai dai a ranar Talata, an hangi Ningi, a harabar majalisar dattawa da ke Abuja a cikin bakar motarsa kirar Toyota Landcruiser Jeep.
A ranar 28 ga watan Mayu ne, majalisar ta sanar da janye dakatarwar da ta yi wa Sanatan.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da janye dakatar da Ningi.
Ya kuma yi fatan Sanatan zai ci gaba da ayyukansa da ya sava ba tare da wasu sharuda ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp