Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya gudanar da bikin Hawan Nassarawa duk da haramta hawan sallah da ‘yansnda suka yi saboda dalilan tsaro.
Hawan Nasarawa muhimmin ɓangare ne na bikin Sallah a Kano, wanda ake gudanarwa a rana ta uku bayan Sallah.
- ‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa
- Dakarun PLA Shiyyar Gabashin Kasar Sin Sun Gudanar Da Atisaye A Kewayen Tsibirin Taiwan
A al’ada, Sarki tare da tawagarsa sukan hau dawakai daga fadarsa zuwa gidan gwamnati domin gaishe da gwamna.
Sai dai a wannan shekarar, Kwamishinan ‘Yansandan Jihar Kano, Ibrahim Bakori, ya hana duk wani hawan sallah, kan cewar akwai barazanar tsaro.
A sakamakon haka, Sarki Sanusi II ya sauya salon hawan da ake yi da dawakai zuwa amfani da motoci.
Sarkin tare da tawagarsa sun fita a ciki jerin gwanon motoci zuwa gidan gwamnati, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya tarbe su.
Bikin bana ma ya sha bamban da na baya, domin an sauya hanyoyin da ake bi a baya.
Duk da hakan, jama’a da dama sun fito suna murna da jin daɗi yayin da motocin Sarkin ke wucewa.
Duba hotunan hawan a ƙasa:
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp