Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya soki matakin Shugaba Bola Tinubu na ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro a faɗin ƙasa, yana mai cewa matakin bai dace ba kuma ba shi ne muhimmin abin da ke magance matsalar tsaro ba.
A hirarsa da Arise TV, Baba-Ahmed ya ce dokar ta-ɓacin da aka sanar ta samo asali ne daga rashin fahimtar ainihin matsalar da ake fuskanta, yana mai bayyana ta a matsayin abin ban dariya da ba zai kawo sauyi ba.
- Zhao Leji Da Wang Huning Sun Gana Da Shugaban Majalisar Dattijan Kasar Madagascar
- Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Alhinin Rasuwar Dattijo, Ambasada Jabbi Maradun
Baba-Ahmed ya yi tir da shawarar gwamnatin tarayya ta dakatar da gina makarantu a yankunan karkara saboda barazanar hare-hare, idan ya bayyana wannan shawara “mai haɗari kuma babban kuskure.” Ya ce yaƙin da malamai da masana ilimi ke yi wajen kare ci gaban ƙasa yana daidai da rawar da jami’an tsaro ke takawa, don haka dakatar da gina makarantu ba zai taɓa zama mafita ba. Ya kuma soki shirin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro 50,000 yana mai cewa matsalar ba ƙarancin ma’aikata ba ce, illa cin hanci da karkatar da kuɗin samar da tsaro.
A cewarsa, idan an rage cin hanci da almundahanar kuɗin tsaro, ƴansanda kaɗai za su iya murƙushe ta’addanci da fashi a cikin makonni biyu. Ya yi watsi da batun samar da masu gadin daji, yana cewa rundunonin tsaron ƙasa tuni suna da ƙwarewa da ƙarfin da ya dace wajen daƙile ƴan bindiga idan aka basu ingantaccen shugabanci na gaskiya. Ya tunatar da irin rawar da Sojojin Nijeriya suka taka wajen daidaita ƙasashen Afrika tun daga shekarun 1970, yana mai cewa rashin tsari ne ya sa matsalar cikin gida ta gagari gwamnati.














