Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya nemi gwamnoni masu barin gado su guji katsalandan a harkokin gudanar da mulki a jihohinsu yayin da suke barin gwamnati a karshen watan Mayu.
Saraki ya bayyana haka ne a taron bikin bankwana da aka shirya wa gwamnonin masu barin gado da masu kama mulki a Abuja, Saraki, wanda tsohon gwamnan Jihar Kwara ne, ya shawarci gwamnoni 18 masu barin gado su rungumi sabon rayuwar da za su fuskanta su kuma shirya bayar da gudummawarsu a bangarorin rayuwa da daban daban.
- Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Soke Nasarar Zababben Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti
- Mutum 2 Sun Shiga Hannu Kan Kisan Ma’aikatan Ofishin Jakadancin Amurka
A sakon fatan alhairi ga gwamnonin, , Saraki ya yaba musu a kan yadda suka bayar da gudumawar bunkasa jihohinsu, sai dai ya karfafa bukatar da su bar gwamnonin da za su gajesu su gudanar da nasu ayyukan ba tare da katsalandan ba.
Ya kara da cewa, “A yayin da kuka kasance ba gwamnoni ba, ku bar wadanda suka gaje ku su yi aikinsu. Ku koma ga iyanlanku, na tabbatar da cewa a halihn yanzu mata da yaranku da jikokinu na nan duk sun kokasa ku koma gida ku yi ta zumunci a tsakaninsu, ku shirya fuskantar wata rayuwa daban, ku yi tanadin kudadenku don kudaden ba za su rinka shigowa kamar da ba.”
Wani tsohon gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu ya nemi sabbi da tsofaffin gwamnonin su muhimmantar da jin dadin al’umma a jihohinsu ba tare da nuna banbanci siyasa ba.
Ya yi gargadi a kan mulkin kama karya, ya ce, irin haka ba zai haifar da da mai ido ba.
“Sau da dama zaka ji wasu na cewa, wannan lokacinmu ne, kada ku yi irin wannan kuskuren, wani tsohon gwamman da ya yi irin wannan ikirarin a yanzu yana can yana yawo a titi.”
Aliyu ya kara da cewa, zamaka gwamna ba yana nufin kai ne ka fi ilimi ko nagarta ba, watakila ma kai ne na karshe a aji a lokacin da kuke karatu amma Allah ya daukaka ka a kan haka kada ku rungumi girman kai a harkokinku.”
Haka kuma tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya nemi tsohofaffain gwamnoni su guji katsalanda a harkokin mulkin jihohin na su, su bar sabbin gwamnoni su yi aikin su ba tare da kawo musu cikas ba, ya nemi su rungumi wasu harkokin da za su taimaki rayuwar su.
Taron ya samu halartar manyan baki da dama, da suka hada da, Kayode Fayemi, Aminu Tambuwal, Aminu Masari, Charles Soludo, Bala Mohammed, Babagana Zulum, Dauda Lawal, Reb Fr Hyacinth Alia da sauransu.