Sarautar Sarkin Musulmi Da Gwagwarmayar Rikon Sarauta (2)

Cigaba daga ranar Alhamis da ta gabata.

 

A farkon shekara ta biyar da hawan sarautar sarkin Musulmi Muhammadu Bello yakai hari Kalabaina, ita kuwa kawa be ga Sarkin Gobir Aliyu.

A wannan yaki ne waba’i mai yawa ya auku, inda mabiyan Muhammadu Bello marasa adadi suka mutu.

A cikin shekarar dai, anyi yaki da Azbinawa har sau biyu.

Haka nan yayi yakin cinye Nabatsame, ya kuma yi yaki da Maraɗi a karo na biyu. Sannan kuma ya kai yaki har Gawakuke.

Akwai daga labarin yakinsa da Azbinawa, inda Sarkin su Ibra da Sarkin Gobir Ali da sarkin Katsina Randa suka gama kai tare dayin shawara a tsakaninsu, suka kudurci kawowa Sarkin Musulmi Muhammadu Bello gagarumin hari.

A lokacin sai suka shiga tattalin yaki, suka shafe watanni uku suna gayyatar dakaru daga sassa mabanbanta, har sai da suka haɗa gagarumar runduna.

Sannan sarkin Azbinawa Ibra ya kwaso rundunarsa ya soma kawowa wasu garu-ruwan Musulmi hari.

A kan haka suka kwace garin Katuru, suka yi murna kwarrai da haka. Tsammaninsu sun hau hanyar da zasuyi galaba akan Muhammadu Bello ne, ashe kuwa tanadi Allah Ta’ala yayi musu. A lokacin kuma, sarki Musulmi na zaune a Wurno ne.

Don haka koda labari ya riskeshi, sai shima ya shiga shirin yaki babba, sannan ya fita daga wurno wata ranar juma’a bayan sallar jumu’a.

Suka fara sauka a Giyawa suka kwana da safe sai gasu a Shinako, sannan suka karasa Lajingo suka kwana biyu.

A cikin Lajingo ne ya haɗu da sarakunan garuruwan hausa na fulani da aka naɗa a gabas, a ciki har da Sarkin Kano Ibrahim Dabo, sun kawo ɗauki ga wannan yaki da za’a nufa.

A wannan wuri kadirawa suka kulla alkawari gaban sarkin Musulmi cewa babu gudu babu ja da baya a wannan yaki, sai dai a mutu. Daga nan runduna ta tashi, babu wanda yasan adadin jaruman cikinta sai Allah. Sannu a hankali suka riski Randata, sannan suka karasa Buleci suka yada zango.

A nan Buleci, Allah ya nuna karamar Sarki Muhammadu Bello, domin sun sauka ne akan wani tudu busasshe wanda babu komai akansa sai ciyayi marasa kyawu da kananun itatuwa A lokacin kuma yanayin zafi ne, don haka kishirwa ta dami mutanen wannan runduna.

Tun a na jurewa har mutane suka fara galabaita, suka soma yanke kaunar rayuwa da tunanin mutuwa, don haka sai akai shawarar a sanar da sarkin Musulmi halin da mutane suke ciki.

Koda aka sanar masa, sai yace “kowannen ku yaje ya gina rijiya a inda ya sauka, insha Allahu zai samu ruwa a ciki.”

Haka kuwa akayi, ruwa ya samu, akasha akayi girki aka baiwa dabbobi, sannan aka yi wanka. Farin ciki da karfin jiki ya dawowa mutane. Akayi ta mamakin karamar Sarki Muhammadu Bello.

A wannan wuri sukayi kwanaki har zuwa daren sallar layya, sannan suka hau dawakai suka cigaba da tafiya, suka sauka a Riyojin Lema, suka yi sansani. Aka hana kowa hura wuta a cikin daren nan.

Da safe suka zabura suka isa Tilla Gawakuke, nan ma sukayi sansani cikin shiri domin sun sani tanan ne Ibra zai fito musu.

Daga kusan wucewar sa’a guda sai ga Ibra da sarkin Gobir Ali da sarkin Katsina Randa da rjndunoninsu sun iso. Rundunoni suka fuskanci juna kafin daga bisani yaki ya ɓarke a tsakaninsu.

Ba a ɗauki lokaci ana fafatawa ba, sai ga Ibra ya ɗafe bisa ingarman dokinsa ya sheka da gudu tsakankanin tudunnai, bai waiwayi saurin kiran mai kira ba. Daga nan fa sai rundunarsu ta watse, kowa ya shiga gudun neman tsira.Rundunar Musulmi suka bisu abaya suna kisan su. An yi wannan abu ranar Talata.

Sarkin Musulmi Allah ya yarda dashi ya kwana biyu anan bayan yaki ya kare, sannan ya tashi izuwa Dutsen Zale, aka kama kafirai kamar dubu aka kashe su da yanka.

Sa’ar nan ya hau ya nufi Gawon Gazau, Musulmi sukayi sansani anan, suka kwana bakwai sannan suka kai hari ga Sarkaki suka ci galaba akanta. A lokacin nan, sai da takai Musulmi suna kwana basu tsoron wani mutum kafiri ko guda ɗaya.

Daga nan sai Muhammadu Bello yayi sallama da Sarakunan gabas yayi musu godiya suka koma garuruwansu, sannan shikuma ya tashi izuwa Lajinge, ya ɗanyi sauraro kaɗan, ya ɗora ɗansa Fodio mulkinta.

Bayan nan, sai ya wuce izuwa Shinako, nan ma ya ɗora ɗansa Aliyu mulkinta, sa’ar nan ya koma wurno da zama. Da Sarkin Musulmi ya sauka gida lafiya, sai ya gode Allah daya mai dashi gida lafiya, ya kumahori Musulmi da kasan cewa masu yawan tuba ga Allah.

Bayan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya huta a gida, sai kuma ya sake ɗaura haramar yaki zuwa Anka a lokacin kaka.

Daya gama haɗa rundunarsa, sai ya fita Wurno, ya riski wani gari Mada-rumfa akan hanya, ya cishi da yaki, ya warwatsa shi, ya kuma kafa ɗansa Ibrahim shugaba a garin.

Sannan ya wuce gaba izuwa Bakura, nan ma ya kwace ikonsa, ya kuma ajiye ɗan ɗan Uwansa Ahmadu shugaba.

Daga nan ya wuce Anka, yayi yaki da ita mai tsanani, ya samu nasara sannan ya koma gida.

An ce Muhammadu Bello yayi yakuna akalla guda 47 waɗanda shine yayi jagorancinsu da kansa yana kan karagar Sarkin Musulmi, amma babu wanda zai iya tantan ce adadin yakunan da akayi a lokacin mulkinsa sai Allah.

Haka kuma an ce bai gushe ba yana yaki don ɗaukaka addinin Allah har saida lamurra suka koma dai-dai kamar sanda Shehu Usmanu yake raye.

Wuraren da Muhammadu Bello ya zaune sune:-

Da fari ya fara zama a Yamulu tsawon shekaru biyu a lokacin shehu na Degel yana ribaɗi, watau kai hare-hare da kuma taryar abokan adawa idan sunzo da hari. Sannan ya zauna a Sokoto nan ma don Ribaɗi, ya kuma zauna Gwandu don Ribaɗi.

A halin sarautarsa kuwa, ya zauna a Karandai, sannan Magarya, sannan wurno, kuma nufinsa ya rasu yana yawo garuruwa domin ribaɗi.

Har ma an jiyoshi yana cewa “Hakika mazaunin ribaɗi, idan ya mutu anan aka turbuɗeshi acikinta, ba za’a naɗe takardar saba. Zai zamo ana rubuta masa lada a kullum kamar yadda ake rubuta masa a lokacin rayuwarsa, daga nan har ranar tashin alkiyama”.

Don haka yayi wasiccin cewa koda ya mutu, kada a binne gawarsa a Sokoto ko kuma awani wurin sai a wurno.

Haka kuwa akayi, ya rasu da marece na ranar alhamis, 25 ga watan Rajab na shekarar 1253 hijiriyya, a wurno.

Maganarsa ta karshe kalimatussashada ce sau uku, sai kuma Ayar Al-kur’ani maigirma.

Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya rasu yana da shekaru 57 da watanni 11. A lokacin kuma yana da shekaru 21 bisa karagar sarkin Musulmi. Don haka a wurno aka binne shi. Kuma har yanzu a can kabarinsa ya ke.

Dafatan Allah ya rahamshe shi. Amin.

Cigaba a gobe in sha Allahu.

Exit mobile version