Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya naɗa sabon Dagacin Janguza mako guda bayan da Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf ya sake naɗa shi a karagar mulki, duk da takaddamar da ake fama da ita kan sarautar Kano.
A ranar Alhamis ne Sarkin ya amince da naɗin Hamisu Sani a matsayin Dagacin Janguza da ke karamar hukumar Dala a jihar, inda ya buƙace shi da ya tabbatar da zaman lafiya tsakanin al’ummar yankin, tare da bayar da gudunmawar sa wajen ci gaban jihar baki daya.
- CJN Ya Yi Sammacin Babban Alkalin Kano Da Alkalin Tarayya Kan Saba Umarnin Kotu
- Rikicin Masarautar Kano: Lauyoyi Da Alƙalai Sun Tozarta Ɓangaren Shari’a – Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi
Tun da farko dai hakimai da manyan mutane da ƙungiyoyin addini da na ƴan kasuwa ne suka yi mubaya’a ga Sarki Sanusi a babbar fadar Kano.
Tawagar ta hadar da shugabannin ƙungiyar Ansaruddeen da Darikar Tijjanniya da ƴan kasuwa daga cikin kasuwar masaƙu tta Kano da Kantin Kwari da kuma ƴan kasuwar kayayyaki ta Singer da dai sauransu.
An sake naɗa Sanusi II a matsayin Sarkin Kano a ranar Alhamis ɗin da ta gabata bayan majalisar dokokin Jihar ta soke dokar Majalisar dokokin Jihar Kano ta baya tare da mata gyaran fuska da Gwamna Yusuf ya sanya wa hannu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp