Sarkin Afaka Ya Jagoranci Tattaunawa Kan Zaman Lafiya

Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna

Masarautar Gundumar Afaka dake  Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, karkashin jagorancin Sarki Sani Musa Umar da hadin gwiwar hadakan kungiyoyin kabilun garin Afaka, sun jagoranci addu’oin zaman lafiya a gundumar na Garin Afaka,  da kuma kara tabbatarwa  Inyamurai cewa su cigaba da harkokin su kamar yadda suka saba.

Taron addu’o’in ya samo asali ne sanadiyar zaman dar-dar da Inyamurai da wasu kabilu dake  zaune a gundumar suke  yi tun bayan da ‘yan ta’addan yankin Inyamurai suka lashi takobin ta’addanci a Kasa.

A Jawabinsa, mai girma Sarkin  Afaka Alhaji Sani Musa Umar, ya bayyana cewa,   “Zaman lafiya shi ne ginshikin rayuwa, idan babu zaman lafiya babu cigaba ga al’umma. Kuma Inyamuran Afaka muna zaman Lafiya da su saboda haka babu wani abin da zai raba kawunanmu.”

Sarki ya yi kira ga Matasa da su guji aikata duk wani abin da zai tayar da da hankalin al’umma,  kuma su zauna lafiya da kowacce Kabila.

Sarkin  ya kara da cewa duk wani motsin da ba a gane ba,  ko kuma alamun wani na shirin tayar da zaune tsaye to ayi gaggawar sanar da hukuma, ko kuma a sanar da shi.

Daga karshe Sarkin  ya yaba wa gwamnatin tarrayya da ta Jiha, sannan kuma ya kara yabawa al’umman yankin Arewacin Kasar nan  dangane  da matakin da suka dauka domin hana daukar ramuwar gayya.

Kabilu da kungiyoyi daban-daban sun samu halartar taron, kuma kowanne wakili na kabila ko kungiyoyi sun tofa albarkacin bakinsu, inda kowa ya goyi bayan zaman lafiya.

A karshe an dauki lokaci mai tsawo ana addu’o’in neman zaman lafiya, wanda malaman addinin Kirista da na Musulmi suka jagoranta, Sannan mai girma  Sarkin Afaka  ya umurci Fastoci da Limamai su ci gaba da yin addu’o’i a Coci da Masallatai domin samun zaman lafiya mai dorewa na har abada.

Exit mobile version