Sarkin Kano Ya Yaba Wa Gwamna Ganduje Kan Kyautata Wa Baki

Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya yabawa Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa kyakkyawan jagorancinsa, musamman yadda ya shigo da sauran bakin abokan zamanmu cikin harkokin gudanar da Gwamnatin Jihar Kano,  Sarkin yayi wannan jawabin ne a lokacin da yake gudanar da wailimar buda baki da aka shirya a fadar Sarkin na Kano ranar 28 ga watan Ramadan na wannan shekara wanda aka shiryawa Gwamna Ganduje da ‘yan tawagar sa.

Malam Muhammadu Sanusi II ya ci gaba da cewar wannan ci gaba ne wanda ke bayar da damar fahimta sauran bakin da muke karbar bakuncinsu, yace ya zama dole muyi jinjina tare da nuna godiyarmu ga Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje  Khadimul Islam bisa ga wannan kyakkayawar aniya, tasa wadda ta inganta kyakkyawar zamantakewa ba tare da la’akari da inda mutum ya fito ba.

Jihar Kano jiha ce wadda ta dade  da kuma sabawa wajen karbar baki  tare da girmama mutane daga duk inda suka fito, yace wannan shi ne kashin bayan  ci gaban da Jihar Kano ke tinkaho dashi, ko shakka babu munyi sa’ar samun mutm irin Gwamna Ganduje wanda ke kulawa da al’amuran Kanawa, a cewar Sarki Malam Muhamamdu Sanusi II.

Sarkin na Kano Malam Muhammadu Sanusi II  ya ci gaba da cewa wannan buda baki shi ne irinsa na hudu tun darewarsa kan karagar sarautar Kano, saboda haka muka gayyato muhimman mutane masu ruwa a tsaki harkokin gudanar da wannan Jiha tamu mai albarka.  Akwai ‘yan siyasa, ‘yan Kasuwa,  Malamai da sauaransu. Sarkinj yace zaku yarda dani idan na ce dukkanmu dake wannan wuri mune kashin bayan ci gaban wannan Jiha. Saboda haka hakkin duk wanda ya halarci wannan buda baki ne  tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa wanda zai kara hada kan al’ummarmu.

Malam Muhammadu Sanusi II ya kuma godewa Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa yakin da take da sha tare fataucin miyagun kwayoiyi a Jihar Kano, don haka sai ya bukaci gwamnatin da ta kara himmatuwa kan wannan babban aiki .

Da yake gabatar  da nasa bayanin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya godewa Sarkin na Kano bisa shirya wannan walimar buda baki, yace ci gaba ne samun irin wannan haduwa da zata tabbatar mana da ci gaban al’ummar Jihar Kano, Bayan ya jinjinawa jami’an tsaro Gwamna Ganduje  ya kuma nemi karin taimakon Ubangiji musamman ganin yadda zaman lafiya ya samu, a Jihar Kano  saboda haka muna kara yiwa Allah godiya kasancewa Jihar Kano , jihar data zarta sauran jihohin tabbaccen zaman lafaiya a Najeriya, inji cewar Ganduje.

Da yake tsokaci akan maganar yaki da sha tare da fataucin  miyagun kwayoyi, Gwamna Ganduje ya tabbatarwa da Sarkin cewar yanzu haka shirye shirye sun yi nisa na hada taron masu ruwa da tsaki bayan sallah  domin kawo karshen wannan bakar al’adar shaye shaye, yace muna yabawa kokarin jama’a bisa bayar da goyon baya ga Jami’an tsaro  domin tabbatar da samun zaman lafiyar  a Jihar Kano.

Exit mobile version