Ahmed Muh'd Danasabe" />

Sarkin Lokoja Ya Nada Sabon Shugaban Masu Magungunan Gargajiyar Lokoja

A jiya Laraba ne Mai Martaba Sarkin Lokoja, Alhaji (Dakta) Muhammadu Kabir Maikarfi III, ya nada sabon shugaban kungiyar masu magungunan gargajiya ta karamar hukumar Lokoja, Alhaji Adamu Muhammed Ibrahim(Nda Bida).

Bikin wanda ya samu halartan kungiyoyin masu magungunan gargajiya daga sassa dabam dabam na karamar hukumar Lokoja da masu rawanin Sarki da abokan arziki da kuma sauran jama’a ma’abota, an gudanar dashi ne a fadar mai martaba Sarkin na Lokoja da misalin karfe 10.30 na safe.

Da ya ke jawabi a wajen bikin nadin, mai martaba Sarkin Lokoja, Alhaji Muhammadu Kabir Maikarfi 111, wanda ya samu wakilcin wazirin Lokoja, Alhaji Abdulrahaman Babakurun, kira yayi ga sabon shugaban kungiyar masu magungunan gargajiyan daya yayi hakuri da jama’a ganin cewa a yanzu yana jagorancin kungiya mai muhimmanci a cikin al’umma. Sarkin na Lokoja har ila yau ya bukace shi da yayi koyi da magabatan kungiyar, wato shugabannin kungiyar da suka rike shugabancin kungiyar a baya.

Kazalika sarkin ya shawarce shi da ya gudanar da adalci a tsakanin mambobin kungiyar domin samun cikakken hadin Kansu.

Alhaji Kabir Maikarfi ya kuma yi kira ga mambobin kungiyar masu magungunan gargajiyar da suyi biyayya ga sabon shugaban nasu tare da bashi hadin kan da ya dace domin bashi daman sauke nauyin data rataya a kansa na jagorancin kungiyar.

Daga nan, sarkin Lokoja ya taya Alhaji Adamu Muhammed Ibrahim murna a bisa nadinsa a matsayin shugaban kungiyar musu magungunan gargajiyar ta karamar hukumar Lokoja.

Da yake zantawa da wakilin jaridar LEADERSHIP A YAU, kadan bayan nada shi,sabon shugaban kungiyar masu magungunan gargajiyar ta karamar hukumar Lokoja, Alhaji Adamu Muhammed Ibrahim, wanda aka fi sani da Nda Bida, ya godewa Allah(SWT) daya nuna masa ranar ta jiya,yana mai cewa rana ce da ba zai taba mantawa da ita ba. Ya kuma godewa mai martaba Sarkin Lokoja, Alhaji Muhammadu Kabir Maikarfi 111, a bisa nada shi sarautar shugaban masu magungunan gargajiya ta karamar hukumar Lokoja.

Alhaji Nda Bida har ila yau ya godewa dukkan wadanda suka yi ta fadi tashi wajen ganin mai martaba Sarkin na Lokoja ya tabbatar masa da rawanin shugaban masu magungunan gargajiyar na Lokoja.

Sabon shugaban wanda tunda farko ya bayyana farin cikinsa, ya kuma yi alkawarin cewa da yardan Allah zai sauke nauyin da Allah(SWT) ya dora masa na ganin yayi adalci ba tare da nuna bambanci ko wariya ba a tsakanin mambobin kungiyar.

Alhaji Nda Bida ya kuma yi addu’a Allah ya jikan wanda ya gaji shugabancin kungiyar daga gare su da kuma sauran magabata da suka koma ga mahaliccinsu.

A karshe ya nemi hadin kan sauran mambobin kungiyar domin ganin ya samun daman sauke nauyin da ta rataya a kansa.

An haifi Alhaji Adamu Muhammed Ibrahim a garin Lokoja a 1973. Ya yi karantunsa na firamare a makarantar firamare ta Bishop Crowther da kuma cibiyar nazarin harshen larabci da islamiya( Markaz) duk a birnin Lokoja.

Exit mobile version