Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar II, tare da Jama’atu Nasril Islam (JNI), sun yi ta’aziyyar rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi, wanda ya rasu ranar Alhamis yana da shekaru 98.
A wata sanarwa da Sakataren JNI, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, ya fitar, ya ce Sheikh Dahiru babban jagora ne kuma ginshiƙi ga addini, kuma rasuwarsa babban giɓi ne.
- Sheikh Zakzaky Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
- Sin Ta Gabatar Da Takardar Bayani Game Da Kayyade Makamai Da Rage Soji Da Hana Yaduwar Makamai A Sabon Zamani
Sarkin ya aike ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, almajiransa, Gwamnatin Jihar Bauchi, jagororin ɗariƙar Tijjaniyya, da ɗaukacin al’ummar Musulmi.
JNI ta bayyana cewa Sheikh Dahiru ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyar da Alƙur’ani da ilmantar da matasa.
Ƙungiyar ta ce rasuwarsa tana tunatar da yadda rayuwa take, don haka ya kamata mutane su tuba, su yi ayyukan alheri, kuma su kasance masu kyautatawa wa juna.
JNI ta ƙara da cewa rasuwar ta nuna ƙarshen wani zamani, tana kuma roƙon Allah Ya gafarta masa, Ya jikansa kuma Ya sanya shi Aljannatul Firdaus.














