Assalamu Alaikum. Barkan mu da sake haduwa, yau ma zan koyar mana da yadda nake awarata kashi na uku. A makon jiya, ya kamata mu ce kashi na biyu, sai muka manta muka ce karo na uku, ajizanci ne irin na dan’adam, a yi mana uzuri.
Wasu na iya cewa, kullum awara? E, awara amma wannan ta musamman ce.
Abubuwa da nake bukata na kayan hadi:
Ina bukatar awara
Attaruhu
Albasa
Kwai
Mai
Dandano
Kabeji
Cucumber
Awara daya idan na yanka ta sai in dauko tukunya in zuba ta in sa mata dandano, in sa ruwa in kunna gas in dora ta idan ta tafasa sai in tace in bar ta ta wuce.
Sai in dauko abin da zan soya in zuba Mai in kunna gas in dora sai Mai ya yi zafi sai in fara suya, idan na gama soya ta sai in ajiye ta a gefe.
Sai in dauko kwaina, ya danganta da yawan awarata sai in fasa, in sa, sai in kada in ajiye a gefe, in dauko Koren tattasaina da na gyara in yanka, sannan in yanka albasa irin yankan da nake so, sai in dan nika attaruhu kadan, sai in kuma dora tukunya ta wadda za ta isa in yi hadin awara a ciki.
Ina fara zuba Mai sai in sa Albasa da Corry in juya, idan ta dan dahu albasar sai in zuba kwai in dan jujjuya, sai in kawo attaruhu, dandano da Koren tattasaina duk in zuba in ci gaba da juyawa har kwan ya dagargaje, idan ya dagargaje sai in kawo awarata in zuba in ci gaba da juyawa, shikenan sai in juye a abin da zan ci, in zuba kabeji da cucumber.
A ci dadi lafya.