Rundunar jami’an tsaro ta hadin guiwa ta Operation Delta Safe (OPDS) ta cafke wani jirgin ruwa mai suna MV Ofuoma da ma’aikatansa, bisa zargin safarar man fetur da aka tace ba bisa ka’ida ba.
Rundunar Sojin Ruwa ta Nijeriya ce ta kama jirgin ruwan a tashar Abonnema Jetty da ke Fatakwal.
Kwamandan OPDS, Rear Admiral Olusegun Ferreira, wanda ya samu wakilcin kwamandan bangaren OPDS, Commodore John Siyanbade ne ya bayyana hakan a jihar Bayelsa.
Kwamandan ya kara da cewa an kama MV Ofuoma ne a ranar 15 ga watan Agusta.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa OPDS za ta ci gaba da aikinta na kawar da satar danyen mai a Nijeriya.