Hukumomin Saudiyya sun saki ‘yan Nijeriya uku da aka tsare a Makka bayan an yi musu cushen ƙwayoyi a cikin jakunkunansu a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano.
Waɗanda aka saki sun haɗa da Maryam Abdullahi Hussaini, Abdullahi Bahijja Aminu, da Abdulhamid Saddiq.
- Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
- Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa
An saki mutanen ne bayan gwamnatin Nijeriya ta shiga cikin lamarin.
Mijin Maryam ya tabbatar da cewa matarsa ta dawo gida, inda ya gode wa NDLEA, jami’an Nijeriya a Saudiyya da kuma sauran masu hannu wajen ceto su.
Maryam ma ta bayyana farin cikinta tare da godewa duk wanda ya taimaka da addu’a.
Hukumar NDLEA ta bayyana cewa wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ce a filin jirgin sama na Kano ta boye jakunkunan ƙwayoyi a cikin kayan matafiyan.
An kama shugaban ƙungiyar, Ali Abubakar Mohammed (wanda aka fi sani da Bello Karama), tare da wasu abokan aikinsa.
Hukumar ta ce mutanen ukun ba su da laifi kuma an zalunce su ne kawai.
An saki su ne bayan bincike da kuma ƙoƙarin diflomasiyya na tsawon makonni.
Lamarin ya tayar da hankali kan tsaro a filayen jirgin sama a Nijeriya da yadda masu aikata laifuka ke amfani da fasinjoji marasa laifi.
Hukumar ta ce za a ɗauki ƙarin matakai don hana faruwar irin wannan lamari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp