Connect with us

KIWON LAFIYA

Shan Magani Lokacin Al’ada Na Hana Haihuwa

Published

on

Kwararriyar likita a kan al’amauran da suka shafi haihuwa na mata, Abosede Lewu ta yi kira ga mata da su rage yawan shan magani dake rage laulayi a lokacin al’ada a cewa yin haka na lalata mahaifar mace.

Lewis wacce Jami’ar kungiyar ‘Keep All Mothers Alive (KAMA)’ ce bayyana cewar yawan shan magani musamman ma ga ‘yanmata wadanda basu haihuwa ba a lokacin da suke haila na iya hana haihuwa.

Ta ci gaba da bayanin cewar” Mafi yawan mata kan yi amfani da wasu kwayoyi a lokacin da suke yin al’ada domin rage radadin al’ada amma kuma hakan babban hadari ga mace domin ya kan lalata mahaifarta ta kafin ta haihuwa a gaba.

Lewu ta yi kira da mata da su daina shan ire-iren wadannan magunguna domin kada su yi masu illa.

 

Hanyoyin Rage Laulayi Da Kuma Radadin Al’ada Ga Mata:

  1. Motsa jiki shi wannan ba sai mace ta tashi tana tsalle-tsalle ba ko kuma guje-guje ba, mace za ta iya motsa jiki a cikin gidan ta, ta hanyar yin aiyukkan cikin gida
  2. Amfani da ruwan zafi; da zarar mace ta fara yin al’ada za rika wanka da ruwan dumi, haka nan kuma ta rika shan shayi mai zafi.
  3. Hutu kamar yin bacci na rage ciwon kai da zazzabin da akan ji a lokacin ake yin haila.
  4. Dabarun bada tazaran hihuwa; Wasu likitoci sun ce amfani da dabarun bada tazaran haihuwa zai taimaka wajen rage laulayin haila.
  5. Cin wasu kayan abinci dake kara wa mutum karfin garkuwa; A lokacin da mace ta fara al’ada kamata ya yi ta rika cin kayan bincike dake dauke da sinadarin inganta garkuwan jiki.Advertisement

labarai

%d bloggers like this: