Bisa yadda lamura suke gudana a halin yanzu, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa (INEC), tana bukatar samun cikakken goyon baya daga wurin masu ruwa da tsaki kafin ta samu hanyar gudanar da sahihin zabe a 2023.
Shekaru da dama ‘yan siyasan Nijeriya suna kokarin bin duk wata hanya domin zama kan karagar mulki tare da amfani da ofishinsu wajen ci gaba da mulkar al’umma.
Sahihin zabe kuma karbabbe ga mutane ya kasance yana da tushe da ke rike da dimokuradiyya a ko’ina a fadin duniya. Sai dai abun takaici a Nijeriya wadannan ginshikai na dimokuradiyya suna nema su zama tarihi.
Rashin tsari da amfani da kudade da akidar jari hujja da rabuwar kawuna da kuma kokarin ci gaba da zama a kan karagar mulki sun jefa siyasar Nijeriya cikin rashin tabbas wanda ‘yan siyasa a Nijeriya suke amfani da su a matsayin makamin zama a kan mulki.
Lallai wadannan rashin tsari a cikin siyasar Nijeriya ba za su iya samar da kyakkyawan gwamnati ba ballantana a samu bunkasan tattalin arziki a cikin kasar nan, domin suna iya zama wani bakan gizo ne da zai iya hadiye ayyukan gwamnatin da za ta hau karagar mulki na tsawan shekaru 10. Alal misali, kamar yadda ‘yan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC suka biya kudin tikitin takara na naira miliyan 100 da kuma ‘yan takarar shugaban kasa karkashin PDP da suka sayi tikitin takara a kan naira miliyan 40.
Akwai abun mamaki a kan haka, ganin yadda mafi yawancin ‘yan Nijeriya da suke fama da yunwa, wanda wadannan kudade zai iya ciyar da su ko da na wata daya ne.
Babban abin takaicin ma dai shi ne, yadda ‘yan siyasa masu neman takara suke raba wa daliget daloli domin su zabe su a lokacin zaben fid da gwani da suka gabata.
Don haka, idan aka duba irin wadannan abubuwa a cikin siyasar Nijeriya akwai abin damuwa a kan ko INEC za ta iya gudanar da sahihin zabe a 2023?.
Idan har ‘yan siyasa za su ci gaba da gudanar da irin wadannan mugayen dabi’u a cikin siyasar Nijeriya, to ta yaya za a iya samun sahihin zabe. Idan har wanda ya ci zabe ba ta hanyar da ya inganta ba, zai kasance manufofinsa da tsare-tsarensa ba za su iya bunkasa tattalin arzikin kasar nan ba.
Wajibe ne sahihin zabe ya kasance wanda mutane suke zabe shi ya samu nasara, a nan dole ne INEC ta ci gaba da samun goyon bayan masu ruwa da tsaki domin samun nasarar gudanar da sahihin zabe a 2023.
Idan aka duba irin matsalolin da kasar nan take fuskanta, zaben 2023 zai kasance mai matukar cike da kalubale ga hukumar INEC.
Miliyoyin ‘yan Nijeriya suna nuna halin ko-in-kula game da zabe sakamakon cewa ko sun jefa kuri’a ba a amfani da ita wajen fitar da sakamakon zabe. Domin haka, sun gunmaci amsar kudade daga hannun ‘yan siyasa kafin su jefa kuri’arsu.
Wasu ‘yan siyasa suna amfani da yakin neman zabe wajen tayar da zaune-tsaye da zai iya kawo hargitsi wanda ke shafar gudanar da sahihin zabe, to dole ne hukumar INEC da dauki mataki a kan haka.
Hakazalika, ko a zaben Jihar Ekiti da gudana sai da jam’iyyar PDP ta yi korafin cewa, APC ta yi amfani da kudi wajen lashe zabe a jihar.
Hukumar INEC ta bayyana sunan dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC, Abiodun Oyebanji a matsayin wanda ya lashe zaben Jihar Ekiti da ya gudana a ranar Asabar da ta gabata.
Shi dai Oyebanji ya samu nasara ne a kananan hukumoni 15 cikin 16 da ke fadin jihar, inda ya samu kuri’u guda 187,057. Yayin da dan takarar da ke binsa, Segun Oni ya samu kuri’u 82,211, sai kuma dan takarar jam’iyyar PDP, Bisi Kolawole ya samu kuri’u 67,457.