Biyo bayan ganawar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi da hafsoshin tsaro a makon da ya gabata bayan hawansa mulki tare da karanta masu karatun-ta-natsu, miliyoyin ‘yan Nijeriya na fatan cewa za a samu gagarumin sauyi kan yanayin rashin tsaro tare dawo da Nijeriya cikin hayyacinta.
Tun bayan da aka rantsar da shi a matsayin zababben shugaban kasar Nijeriya na 16, Tinubu ya dai gaji tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Bayan rantsar da shi, wata tambaya daya ke ci gaba da yawo a zukatan ‘yan Nijeriya da dama shi ne, Shin ko Tinubu zai iya cika alkawarin da ya dauka na magance matsalar rashin tsaro da kasar nan ke fama da shi.
- Jami’an Amurka Ba Za Su Iya Dakatar Da Matakan Sulhu Na Kasashen Yankin Gabas Ta Tsakiya Ba
- Tinubu Zai Gana Da Zababbun Sanatoci A Gobe Alhamis
Bisa kididdigar kashe-kashen da aka yi a Nijeriya da wata cibiyar bincike ta Amurka ta fitar, ya nuna cewa an kashe akalla mutane 89,920 a Nijeriya sakamakon tashe-tashen hankula a cikin shekaru bakwai na farko na gwamnatin Buhari daga Mayu 2015 zuwa Mayu 2022.
Ita ma wata kungiya da ta sadaukar da kai wajen bin diddigin tashe-tashen hankula a Nijeriya ta fitar da rahotonta na shekarar 2023, wanda ya nuna cewa an kashe mutane 1,230 a kasar a rubu’in farko na shekarar 2023.
Rahoton ya kuma ce jami’an tsaro 79 ne suka mutu a cikin wannan lokaci, yayin da aka yi garkuwa da mutane 658 a fadin kasar.
ko bayan rantsar da Tinubu an ci gaba da kashe mutane tare da yin garkuwa da wasu da dama a cikin Nijeriya.
A daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya hau kan karagar mulki, idanun ‘yan Nijeriya sun koma kansa tare da yi masa fatan alkairi na ganin ya magance kalubalen da ke gaban kasar nan, nusamman ma a bangaren tsaro. ‘Yan Nijeriya dai na sha’awar samar da kasa mai cike da tsaro, domin su samu nasarar yin barci da idanuwansu guda biyu ba tare da wata fargaba ba.
Bisa kudurinsa na magance tsaro, Tinubu ya yi ganawarsa ta farko da hafsoshin tsaron kasar nan, inda ya bayyana musu cewa bu sauran bayar da uzuri a bangaren jami’an tsaro.
Ya kuma bayyana musu cewa ba zai yarda da halin da al’ummar kasa ke ci gaba da raguwa ba. A cewar shugaban, a yanayin da yake ciki a halin yanzu, dole ne a hada kan tsaron kasa wajen ceto kasar nan.
Shugaban ya umarci hukumomin tsaro da su fito da wani tsari na magance matsalar rashin tsaro a Nijeriya. Ya ce ba shi da isasshen lokaci dole ne a gudanar da sauye-sauyen da suka dace da wuri-wuri.
Taron wanda shi ne na farko da hafsoshin tsaro, ya kasance karkashin jagorancin babban hafsan tsaro, Janar Lucky Irabor. Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya da babban hafsan sojin ruwa, Bice Admiral Awwal Gambo da shugaban hafsan sojan sama, Air Marshal Isiaka Amao da babban sufetan ‘yansanda, Usman Alkali Baba.