Darakta Janar na hukumar kasuwanci ta duniya (WTO), Dakta Ngozi Okonlo-Iweala ta ce Nijeriya na bukatar bullo da shirye-shiryen da za su taimaka wa al’umma wajen samar da ayyukan yi ga matasa da mata.
Okonlo-Iweala ta bayyana hakan ne da take yi wa manema labarai jawabi a fadar shugaban kasa bayan ganawarta da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata, ta ce bullo da shirye-shirye na al’ummar kasa zai magance wasu matsalolin da ke addabar ‘yan Nijeriya a halin yanzu.
- Gwamnatin Gombe Za Ta Dauki Sababbin Ma’aikatan Lafiya 200
- Fasahar Zane-zane Na Iya Bunƙasa Samar Da Kuɗaɗen Waje Ga Nijeriya – CIS James
“Mun ga shugaban kasa, kuma mun tattauna kan yadda za mu tallafa wa ‘yan Najeriya a wannan lokaci na bukata. Duk mun san cewa ‘yan Nijeriya na cikin matsanancin halin, kowa yana kokawa. Hakan ne ma ya sa na kawo wannan ziyara da kaina. Wannan ba aikin WTO ba ne a hukumance, amma mun sami damar tattaunawa da shugaban kasa kan irin shirye-shiryen da za a iya yi don tabbatar da cewa ana rage radadin da’yan Nijeriya ke sha.
“Mun gudanar da tattaunawa mai matukar muhimmanci kan kokarin bullo da tsare-tsare da za su taimaka wa al’umma wajen samar da ayyukan yi ga matasa, kuma tallafa wa mata da kananan yara, wadanda za su rage wasu wahalhalun da ake fama da su a cikin kasa.
“Mun yi magana na tsawon lokaci, muna bukatar samun damar saka hannun jari da Nijeriya za ta iya dogaro da kanta, ciki har da habaka masana’antar sarrafa magunguna. Mun kuma yi magana kan irin tallafin da hukumar kasuwanci ta duniya za ta iya kawowa.
“Mun yi aiki a Nijeriya tare da mata, musamman wadanda suka mallaki kanana da matsakaitan masana’antu don kokarin taimaka musu wajen inganta kayayyakinsu ta fannin noma, masaku da sauran fannoni domin su samu damar sayar da su da daraja a kasashen duniya.
“Muna kokarin taimaka musu ta fannin fasahar zamani, domin mu horar da matan Nijeriya da masu kananan sana’o’i da matsakaitan masana’antu wajen kara habaka kasuwancinsu da samar da ayyukan yi.
“Abin da muka tattauna da mai girma shugaban kasa kenan a matsayina ta darakta janar ta kungiyar kasuwanci ta duniya, za mu yi kokarin iya bakin kokarinmu don tallafa wa ‘yan Nijeriya a wannan lokaci,” in ji ta.
An Cafke Masu Safarar Kwaya 214 Cikin Wata Bakwai A Gombe
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa reshen Jihar Gombe, ta ce ta kama mutum akalla 214 da take zargi da laifin safarar miyagun kwayoyi a jihar tsakanin watan Janairu zuwa Yuli.
Haka nan, an kama ‘Cannabis Satiba’ mai nauyin kilo giram 93.95, da kuma Kilo giram 257.5 na abubuwan da suka shafi ‘Psychotropic’ da Methamphetamine daga hannun wadanda ake zargin a wannan lokaci.
Kamfanin Dillancin Labarun Nijeriya ya ruwaito cewa Mataimakin Kwamandan Hukumar na Jihar, Bello Mumini ne ya bayyana hakan a wani taro da kungiyar kwararrun masu ba da shawara a Nijeriya ta shirya.
Da yake gabatar da kasidarsa mai taken “Halin da ake fama da shi game da ta’ammali da muggan kwayoyi a Jihar Gombe,” Mumini ya ce wadanda ake zargin 214 sun hada da maza 200 da mata 14.
Ya ce daga cikin mutum 214 da aka kama, 137 daga cikinsu an gurfanar da su a gaban kotu.
Jami’in Hukumar na NDLEA, ya yi tir da yadda ake fama da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar, inda ya kara da cewa hakan yana tasir a tsakanin jinsi, cikin shekaru da kuma yin illa a zamantakewar al’umma.
Ya ce abin takaici ne yadda ake samun mata da dama suna shiga harkar shan miyagun kwayoyi a jihar.
Ya kuma ce abin takaici ne da ya zamto ba a yin amfani da cibiyar gyaran hali ta NDLEA a jihar yadda ya kamata duk da yawaitar shan miyagun kwayoyi a jihar.
Ya ce, “Cibiyar gyaran hali ta NDLEA tana aiki amma ba a amfani da ita kamar yadda ya kamata.
“Muna da daki mai gadaje 24 amma mafi girman abin da muke samu shi ne mutum bakwai da ake tsarewa domin kula da gyaran hallaya da dabi’unsu.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa nake kira ga gwamnatin jihar da gwamnatin tarayya da su tallafa wa cibiyar tare da tallafa wa ake kai wa wurin don inganta rayuwarsu.”
Mumini ta yaba wa kungiyar ta APROCON bisa gudanar da gangamin yaki da hana shaye-shayen miyagun kwayoyi a yayin da take yi wa matasa nasiha akan illar shan muggan kwayoyi da sauran abubuwan sa maye.
A nata bangaren, Shugabar Kungiyar ta APROCON, Dakta Habiba Isah, ta ce shaye-shayen miyagun kwayoyi ya zama wata barazana da ya kamata ta da mu da duk masu ruwa da tsaki mu shigo ciki domin ganin an magance irin illar da ke tattare da ita da kuma rayuwar matasa.
Ta ce kungiyarta ta kaddamar da yaki da wannan barna kuma za ta je wasu manyan makarantun jihar domin jawo hankalin matasa da kuma hana su shan miyagun kwayoyi ta hanyar nusar da su hanyoyin illar abin.
Isah, wacce kuma ita ce Shugabar Sashen, Gidauniyar Ilimi ta Tsangayar Ilimi ta Jami’ar Jihar Gombe, ta bukaci iyaye da su yi taka-tsan-tsan tare da kare ‘ya’yansu daga shan ta’ammali da miyagun kwayoyi.