A ci gaba da kokarin dakile yawaitar samun rikice-rikice a tsakanin manoma da makiyaya, musamman a Arewacin Nijeriya; a watan Yulin 2024, gwamnatin tarayya ta kaddamar da sabuwar ma’aikatar bunkasa kiwon dabbobi.
Haka zalika, domin dakile kaluabelen da ake fuskanta tare da bunkasa fannin na kiwo; Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya kafa kwamitin mutum 23 don bayar da shawarwari ga sabuwar ma’aikatar ta bunkasa kiwon dabbobi.
- Kashi 67 Cikin 100 Na Ɗaliban Kaduna Sun Samu Nasara A WAEC – Kwamishinan Ilimi
- Ronaldo Da Messi Ne Kan Gaba A Jerin ‘Yan Wasan Da Suka Fi Karbar Albashi
Ko shakka babu, wannan fanni na kiwo a fadin Nijeriya na matukar bayar da gagarumar gudunmawa, wajen kokarin ci gaba da wadata wannan kasa da abinci.
Sai dai, daya daga cikin manyan kalubalen da fannin ke ci gaba da fuskanata a fadin kasar shi ne, yawan samun rikici tsakanin manoma da makiyya, wanda hakan ke ci gaba da shafar ayyukan aikin noma na kasar.
Wani rahoto na Afirka da ke bibiyar hada-hadar kasuwanni da kuma fannin tsaro (SBM) ya bayyana cewa, sama da manoma 1,356 ne suka rasa rayukansu a Arewacin Nijeriya, sakamakon hare-haren ‘yan bindigar daji a tsakanin 2020 zuwa 2024.
Wadannan rikice-rikice da aka saba yi shekaru da dama, sun haifar da rikici iri-iri tare da tarwatsa al’umma daga matsugunansu da kuma lalata gonakai da dama.
Jaridar BusinessDay’s, ta yi nazari a kan shawarwarin da kwamtin ya bayar da suka hada da:
1- Kirkiro Da Shirin Zaunar Da Makiyayan Wuri Guda:
Akwai bukatar jawo makiyayan a jiki tare da taimaka musu, domin su rungumi tsarin kiwo na zamani.
Kwamitin ya kuma bayar da shawarar kirkiro da warin kiwo na zamani, musamman domin a zaunar da makiyayan wuri guda.
A cewar kwamtin, ya kamata a fara gyaran kowane wajen kiwon, wanda hakan zai taimaka wajen tattara makiyayan wuri guda.
Ya kuma kamata a samar wa da makiyayan dabarun zamani kan yadda za su rika kula da dabbobinsu.
2- Bunkasa Hada-hadar Kasuwancin Sayar Da Naman Shanu Da Madara:
Kwamitin ya sanar da cewa, ta hanyar samar musu da wajen yin kiwo na zamani, hakan zai taimaka wa makiyayan wajen hada-hadar kasuwancin sayar da naman dabbobinsu da madara da kuma noma abincin Shanunsu da kwamda suke bukata; don ciyar da iyalansu.
A cewar rahoton, za a iya samun nasara akalla a jihohi 20; kuma a cikin shekaru biyar, domin samar da akalla wajen kiwo 5,000; wanda za a ajiye Shanu 50 a cikin kowanne, wanda kuma hakan zai sanya a samar da madara da dabbobin da za a yanka a karkashin shirin.
3 Hada-hadar Kasuwancin Fatar Shanu:
Kwamitin ya bayar da tabbacin cewa, zai magance kalubalen da ake fuskanta a fannin hada-hadar Fatar Shanu; ta yadda za a rika samar da kudaden shiga a fannin.