• English
  • Business News
Saturday, June 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shehu Ibrahim Inyass: Gwarzon Musulunci A Karne Na 20 (II)

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
2 years ago
in Dausayin Musulunci
0
Shehu Ibrahim Inyass:  Gwarzon Musulunci A Karne Na 20 (II)
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shehu Ibrahim (RA) ya taimaki addini da kayan zamaninsa da ya tarar wanda Turawan mulkin mallaka suka yi amfani da su. Shi ne farkon Musulmin da ya yi haka. Ya yi amfani da Rediyo, da Tarho, da Rikoda, da Kamara wajen isar da sakon Musulunci. Don har yau, akwai gidahumin musulmin da yake ganin yin hoto kafirci ne, amma Shehu Ibrahim ne ya wayar mana da kai a kan amfani da wadannan kayan a cikin addininmu na Musulunci. Haka nan amfani da motoci da jirgin sama, da lasifika, da agogo, da zuwa asibitoci.

Shehu Ibrahim yana daga cikin wadanda ya tilasta wa almajiransa zuwa asibiti wanda a da ba a yarda da hakan ba. Sannan ya koyar da yin karatu irin wannan da ake yi na zamani a makarantu.

  • Ganin Girma Da Kwarjinin Annabi (SAW)

Shehu Ibrahim (RA) shi ne farkon Musulmi kuma Malami da ya waye ya san cewa “technology” ba kishiyar addini ba ne. Shi ne farkon malamin da ya yarda cewa Turawa sun je duniyar wata a shekarar 1969 (combo apolo 11) har ma ya yi littafi a kan wannan. Kuma ya yi wa shugaban Amurka na lokacin wasika a kan wannan (documents suna nan a kan haka). Su Malaman Saudiyya cewa suka yi ma duk wanda ya yarda cewa an je duniyar watan kafiri ne, su kuma na Azahar (Misra) suka ce sam ma ba zai yiwu ba.

Amma Shehu Ibrahim ne ya gamsar da su (da hujja) har suka yarda da abin.
Shehu Ibrahim (RA) ya kewaya kasashen duniya har Chana, Beijin, Honkon, da sauran sassan karshen Asiya don taimakon Musulunci. Ya hada kan Musulmi Larabawa da Bakar Fata. Yana da kishi na hakika a kan addininsa na Musulunci mai tsafta ba na ta’addanci ba.

Shehu Ibrahim (RA) yana da kishi a kan Afirka. Ya yi tsayuwar daka tare da ba da gudummawa ga samun ‘yancin duk wata kasa ta Afirka ciki har da kasarmu Nijeriya. Yana da kishin mutane bakar fata ‘yan’uwansa.

Labarai Masu Nasaba

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (3)

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (1)

Bayan haka, Shehu Ibrahim (RA) ne gwarzon namijin da ya tsaya shi kadai ya kori Isra’ila daga kasarsa Senigal wanda nan ne hanyar shigowa Afirka. A lokacin, Faransa ta yiwa Yahudawa izinin shiga Afirka ta Senigal ba tare da takardar biza ba ma. Ba domin Shehu Ibrahim ya kore su ba da mu ma yanzu abin da yake samun Palasdinawa ya same mu. Jamilu Arif, wani danjarida na kasar Misra ya fadi wannan.”

Da yake duniya ta bunkasa da kakkafa kungiyoyi don cimma abubuwa da dama da aka tasa a gaba, Sayyid Isma’il Maidiwani ya yi bayanin cewa Shehu Ibrahim ya ba da gudummawa ta wannan fuskar don ci gaban Musulunci.

Shehu (RA) ya ba da gagarumar gudummawa wajen kafa Rabida ta Malaman Musulunci na Duniya (duk akwai hujjoji a kai a hannu). Sannan ya kafa hadin kan Afirka wanda ta hannunsa ne shugabannin Afirka suka karbi wannan. Ya kuma kafa kungiyoyin da za su taimaki addini irin su Ansarid Dini tare da umurtar almajiransa su kafa, mu nan a Nijeriya akwai Fityanul Islam.

Manyan ‘yanjarida na duniya Turawa da Larabawa da sauran su duk sun yi magana a kan Shehu Ibrahim (RA). Ustazu Abdulkareemin Niyazi ya yi magana a kan Shehu da irin kokarinsa a Jaridar Saudiyya. Haka nan Jamilu Arif na Misra ya yi magana a kan Shehu. Sannan babban malamin Saudiyya Sheikh Muhammad Mahmud Sauwaf a cikin littafin da ya yi mai suna “Yawona Zuwa Kasashen Musulunci” ya yi magana a kan Shehu (RA).

Shehu Ibrahim ne malami bakar fata da ya samu daukakar yiwa Musulmi Sallar Jumma’a a Jami’ar Az’har ta Misra a 1961, wanda kafin shi ba a taba yin wannan ba (RA).

Haka nan ya rike mukamai da yawa a duniya. Shehu ne na Musulunci wanda yake da fahimtoci a cikin Tauhidi, ya warware abubuwan da ya gagari malamai a cikin Tauhidi cikin sauki. Daga cikin mukaman da ya rike a duniya akwai shugaban hadin kan Jami’ar Kairawani da Jami’ar Az’har. Sannan ya rike mataimakin taron Musulunci da aka yi a Karachi ta Pakistan. Yana daga cikin kwamitin da ya kafa Rabida ta Malaman Musulunci na duniya a Makka. Sannan yana cikin kwamitin da ya hada kan jami’o’in Musulunci na duniya a Ribad na Moroko.

Haka nan yana daga cikin babban kwamitin malamai masu yiwa abubuwa hukunci a Musulunci na Misra. Ya rike babban matsayi a taron shekara-shekara na bincike a cikin Musulunci a Misra. Har ila yau, yana da matsayi babba a Majalisar Musulunci ta Jaza’ir da sauran su da dama.

Shehu Ibrahim (RA) ya ci nasara wajen yin kira zuwa shiga addinin Musulunci da hikima da wa’azi mai kyau da jayayya mafi kyau. Idan muka ce Musulunci ma’ana ya hada da Musuluncin, da Imani da Ihsani kamar yadda Hadisin Annabi (SAW) ya fada a Hadisin Jibrilu.

Ba a dinga daukar bangaren Fikhun addini kadai a bar sauran ba kamar yadda ta ke faruwa a wannan zamanin, sai mutum ya hada duk gaba daya.

Amma idan mutum ba zai iya hadawa ba, ya tsaya wa Fikhun addini na makamul Islam din kawai amma kuma ya san cewa akwai karatun Imani na ilmud Tauhidi ba adadi a gabansa da bai sani ba, ballantana kuma ilmut Tasawwuf na Ihsani.

Babban makaminsa na wannan aikin shi ne tsoron Allah, da ilmi sannan ya fahimci zamaninsa (wannan nukuda ce babba). A takaice dai kowa ya tabbatar ba a taba yin Gwarzon Namiji a Musulunci ba irin Shehu Ibrahim (RA) a karne na 20, ba mu Afirka ba har da kasashen Larabawa. Ya bunkasa ilmin addini da Luggar Larabci a Afirka wanda duk ga ‘yan jami’a nan suna ta amfani da karatuttukansa. Bayan wannan, ya watsa ‘ya’ya da jikokinsa da almajiransa a kasashen Turai suna musuluntar da su tare da karantar da su. Tun komawarsa ga Allah har yau; har abada duk wani abu mai amfani za ka ga imma dai ‘ya’yansa ko jikoki ko almajiransa ne suke jagoranci a kai.

Shehu ya kafa alheri, ya yada alherin amma sai aka zo da kishiyarsa, zuwa da kishiyoyinshi abubuwan da ya kafa ne ya kai Afirka cikin bala’in da ake ciki. Amma yanzu da yake an ce ana so a gyara, to lallai a dawo da wannan alheri da kwarewa da cin nasarar da Shehu ya yi, idan aka yi haka da albarkar Annabi (SAW) sai a samu nasarar da ake bukata.

Rikicin wadanda ba su fahimci Shehu Ibrahim Inyass ba kawai ya ta’allaka ne a kan kin tsayawa a matakin ilimin da suke da shi, inda suke kutsawa cikin fannoni ko matakan addini da ba su san komai a kai ba, “suna matakin Fikhun Musulunci amma sai su rika tsallakawa Matakin Imani na Tauhidi ko Ihsani na Sufanci su rika cewa “ya fadi kaza a wuri kaza” alhali ba su da ilmi a kai kwarai da gaske.

Da kowa zai yi adalci ya tsaya a fanninsa sannan ya dauki karatun da Shehu Ibrahim ya yi a kan wannan fannin, da ya san Shehu Shehinsa ne don ya karantar da shi a fannin nasa ma. Haka nan Shehu Ibrahim ya kawar mana da kabilanci a tsakaninmu tare da yaukaka zumunci na ‘yan’uwantaka wanda hatta makiyinsa ma ya yi ma sa shaida a kan wannan. Ko a kan haka, ya dace kwarai da gaske mu rika yin Mauludin Shehu Ibrahim (RA).


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Shugaban Belarus: Amurka Da Kasashen Yamma Suna Kawo Tarnaki Ga Tattaunawar Lumana Tsakanin Rasha Da Ukraine 

Next Post

Bayani A Kan Starlink, Da Yadda Tsarinsa Ya Ke (Kimiyya)

Related

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (3)
Dausayin Musulunci

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (3)

1 day ago
Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (1)
Dausayin Musulunci

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (1)

2 weeks ago
Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci
Dausayin Musulunci

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci

3 weeks ago
Shimfida A Kan Aikin Hajji Da Bayani A Kan Mikatin Da Manzon Allah (SAW) Ya Sa
Dausayin Musulunci

Shimfida A Kan Aikin Hajji Da Bayani A Kan Mikatin Da Manzon Allah (SAW) Ya Sa

1 month ago
Ramadan
Dausayin Musulunci

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (4)

1 month ago
Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (3): Shari’ar Manzon Allah (SAW) Ta Zo Da Wayewa A Kowane Fanni
Dausayin Musulunci

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (3): Shari’ar Manzon Allah (SAW) Ta Zo Da Wayewa A Kowane Fanni

2 months ago
Next Post
Bayani A Kan Starlink, Da Yadda Tsarinsa Ya Ke (Kimiyya)

Bayani A Kan Starlink, Da Yadda Tsarinsa Ya Ke (Kimiyya)

LABARAI MASU NASABA

Aikin Ba Da Ilmi Ba Makamin Takarar Jam’iyyu Ba Ne

Aikin Ba Da Ilmi Ba Makamin Takarar Jam’iyyu Ba Ne

June 7, 2025
Hukumar NPA Ta Bayar Da Kwangilar Aikin Ruwa Na Tashar Lekki

Hukumar NPA Ta Bayar Da Kwangilar Aikin Ruwa Na Tashar Lekki

June 7, 2025
Roland Busch: Kasar Sin Tana Daya Daga Cikin Kasuwanni Mafi Kuzari A Bangaren Kirkire-kirkire A Duniya

Roland Busch: Kasar Sin Tana Daya Daga Cikin Kasuwanni Mafi Kuzari A Bangaren Kirkire-kirkire A Duniya

June 7, 2025
Gwamnatin Tarayya Da Hadin Gwiwar IFAD Za Su Yi Wa Manoma Rijista Domin Tantance Su

Gwamnatin Tarayya Da Hadin Gwiwar IFAD Za Su Yi Wa Manoma Rijista Domin Tantance Su

June 7, 2025
Dalibai Sama Da Miliyan 13 Ne Za Su Rubuta Jarrabawar Shiga Jami’a Ta Kasar Sin

Dalibai Sama Da Miliyan 13 Ne Za Su Rubuta Jarrabawar Shiga Jami’a Ta Kasar Sin

June 7, 2025
Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Na Ganin Tattaunawa Da Hadin Gwiwa A Matsayin Hanyar Warware Takaddamar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Na Ganin Tattaunawa Da Hadin Gwiwa A Matsayin Hanyar Warware Takaddamar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

June 7, 2025
Sojojin Sama Sun Tarwatsa Maɓoyar Ƴan Ta’adda, Ya Daƙile Hari Ranar Idi A Borno

Sojojin Sama Sun Tarwatsa Maɓoyar Ƴan Ta’adda, Ya Daƙile Hari Ranar Idi A Borno

June 7, 2025
shehu ibrahim inyass

2027: An Yi Kira Ga Masu Mulki Da Su Rungumi Tafarkin Inganta Rayuwar Al’umma

June 7, 2025
Tottenham Ta Raba Gari Da Kocinta Ange Postecoglu

Tottenham Ta Raba Gari Da Kocinta Ange Postecoglu

June 7, 2025
Tufka Da Warwarar INEC Kan Yiwuwar Zaben 2023

Ana Ci Gaba Da Samun Rudani Yayin Da INEC Ta Jinkirta Rajistar Sabbin Jam’iyyu

June 7, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.