Tsohon Sanatan Kaduna tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana rashin amincewarsa da maganar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, na ba ‘ya’yansa shawara da su mayar da martani idan mijinsu ya mare su. Shehu Sani, a cikin wani rubutu na Facebook, ya yi kira da a dakatar da ingiza tashin hankali a cikin mu’amalar aure.
Sani ya jaddada muhimmancin maganar azancin ta idan rai ya ɓaci bai kamata hankali ya gushe ba kuma warware matsaloli cikin lumana a cikin gidaje ya fi.
- Yadda Aka Nada Ni Garkuwan Yammacin Ƙasar Nan – Alhaji Shehu
- Shehu Sani Ya Yi Wa DSS Shagube Kan Zargin Kafa Gwamnatin Wucin Gadi
“Sarki Sanusi bai kamata ya ƙarfafa irin wannan nau’in tashin hankali na dukan juna ba. Miji da mata su koyi sarrafa kansu a lokacin fushin da shaiɗan zai kawo cikin gidansu.”
Tsohon Sanatan ya bayar da shawarwari na magance fushi da kuma kauce wa tashin hankalin da ke faruwa a gidaje.
Sani ya ce idan mijin yana cikin fushi, ya kamata ya fita daga gida sannan ya dawo daga baya. Haka ma matar na iya jinkirta magana idan mijinta yana fushi kuma yana magana yana ɗaga murya.
Ya kara da cewa kalmar “Yi hakuri” na da wani tasiri wanda zai iya kawar da shaidan a cikin gida, kuma tashin hankali da mayar da martani na iya kashe aure ba tare da kome ba.