Shugaban Hukumar Duba-gari ta kasa, Dakta Yakubu Muhammad Baba ya bayyana yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karfafa ayyukansu ta hanyar sanya hannu a sabuwar dokar kula da muhalli a Nijeriya, a tattaunawarsa da Editanmu Bello Hamza, ya yi bayanan yadda suke gudanar da ayyukansu har ma da yadda cutar korona ta sauya fasalin ayyukan kula da muhalli gaba daya da irin gudummawar da suka bayar wajen dakile cutar, ga dai yadda hirar ta kasance:
Wani sauyi aka yi wa Hukumar Duba-gari ta Nijeriya?
Kamar dai yadda ka yi magana, mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin yanayin tsare-tsaren gyaran mulkinsa ranar a 6 ga watan Agusta ya sa hannu a sabuwar doka da ta gyara fasalin ayyukan Duba-gari na Nijeriya baki daya. Ya sanya muka canza suna; a da abin da dokar mu ta kayyade mu yi shi ne mu yi rijista ma ma’aikatanmu da suke aiki a fadin Nijeriya. Sannan mu tsara musu dokokin yanayi na koyarwa da fahimtarwa da yadda za su yi aikinsu. To shugaban kasa Muhammadu Buhari ya canza mana suna kuma ya kara mana abin da Bature yake cewa ya kara bunkasa aikin duba gari a Nijeriya da ya sanya wa hannu a sabuwar doka.
A takaice ya kara muku karfi n gwiwa?
Lallai ya kara mana karfi, yanzu ana kiran sunan wannan ma’aikata tamu ‘Enbironmental Health Council of Nigeria’. Su wadannan ayyukan muhalli kamar yadda kuka sani ba wai a Nijeriya kadai ake yin su ba. Hukumar Lafiya ta Duniya, ita ta yi bayani a kan cewa wanne aiki ne ake kira aikin duba gari a duniya baki daya. Ayyukan kuma wanda ita hukumar lafiya ta duniya ta yi bayani da turanci sune ana kiransu ‘components. Su wadannan ‘components’ yanzu sun zama guda ashirin da hudu (24). Cikin ashirin da hudu akwai abin da ake cewa ‘House to House inspection’ ko ‘Housing inspection’. Duba lafiya na gidaje, gidajen nan kuma za su iya kasancewa gidajen zama na al’umma ne ko kuma Ofis ne, a’a ko kuma gidan abinci ne, ko kuma a’a otel ne. Sannan akwai abin da ake cewa ‘International Health Control’, wato duba lafiya na shiga da fice. Saboda su cututtuka ba su da ‘boundary’. Shiyasa a duniya ko’ina ka je za ka ga ma’aikacin duba gari shi za ka fara samu ‘at the point of entry’. Ko dai ta kasa ne, ko ta ruwa ne ko ta sama ne, shi zai fara ganinka.
Idan ya ganka zai duba ya ga ya yanayin lafiyarka, ya zafin jikinka, shi ne daya daga cikin abin da dokarmu ta ce mu yi. Na uku shi ne akwai dokar kula da abinci. Kamar yadda ka sani NAFDAC dokarsu an ce ‘Food and Drug’. To ‘food’ din da NAFDAC suke lura da shi shi ne duk wani abincin da aka yi ‘packaging’, a cikin ‘package’ na su ne. Duk abincin da aka dafa shi a ‘restaurants’ da wanda aka dafa a otel wannan abin duka ‘public health responsibility’ ne. Wanda aiki ne na duba gari.
Idan muka dawo batun barkewar cutar ko kuma cututtuka masu yaduwa, akwai batun annobar korona wanda yanzu an shekara uku ke nan cif da ta shigo tarayyar Nijeriya, wanda kuke ta fadi tashi domin ganin an dakile ta, ya zuwa yanzu ina aka kwana ne batun ayyukan da kuke yi?
Shi dama akwai abin da muke cewa a yanayin tsari na koyarwarmu ‘epidemiology 101’. A cikin wannan tsari na mu shi yake tabbatar mana da cewa akwai cututtuka da ake ce musu ‘imaging and re-imaging diseases’ wato cututtuka ne masu bijirowa sannan za su sake bijirowa. To ina koronabairos tana daya daga cikin ‘classification’, kayyadaddun cututtuka da aka sa su a cikin ‘imaging’ da kuma ‘re-imaging diseases’. Lokacin da korona ta zo ta zo ne a ‘imaging disease’ wanda ba a taba samun annoba ba da ya shafi ‘pandemic’. Idan an ce cuta ‘pandemic’ ana nufin wannan cutar tana ta shafi ko’ina a duniya. Annoba ta duniya shi ake kira ‘pandemic’. Kuma wato hasashe da aka yi na masu kimiyya da kasashen da ake kira ‘debeloped countries’ sun yi ‘anticipating’ cewa ita wannan cuta din idan ta shigo Afrika ta’adin da za ta yi ba a taba gani wanda Bature yake cewa; ‘unprecedented’ amma ‘unfortunately for Africa and in particular for Nigeria’ lokacin da annobar ta zo, dukkanin masu ruwa da tsaki a bangaren lafiya an yi kokarin kulla alaka. Kowa ya zo ya sanya hannu muka yi kokari muka rage abin da Bature ke kira ‘morbidity’ da kuma mortality’ na ‘disease’ din. ‘morbidity’ wanda za su mutu sakamakon cuta din. mortality’ wadanda za su kamu da cuta din.
Alhamdulillahi dukkanin ma’aikatan duba gari na kasa a karkashin ofishina da kuma karkashin Minista a wancan lokacin, Dakta Mahmood Abubakar, mun yi ‘actibating what we called emergency bolunteer scheme’ saboda na daya; idan annoba ta zo kamar yaki, idan yaki ya zo ko mutum ya yi ritaya in dai tsohon soja ne, ana kiransa ya dauki bindiga saboda a tafi fagen fama. Abin da ya faru ke nan a yanayin yaki na korona da ya zo. Minista ya kira harda tsofaffin duba gari da suka yi ritaya, sun taho muka zauna muka yi aiki tare da su. Kuma ina shaida maka cewa abin da muka ba da gudummawa shi ne abin da ake cewa ‘non-pharmaceutical’ ‘non-medical containment strategy’. Abin da muka yi ‘putting’ ke nan. Su kuma wannan ‘non-pharmaceutical measures’ din sune; na farko; ‘enforcement’ na ‘social distancing’. Tabbatarwa da ana amfani da ‘hand sanitizer’ a wuraren da jama’a suke taruwa.
A baya duk kun bi hanyoyin da za ku bi wajen fadakar da mutane; batun wanke hannun nan, batun rashin cudanya, batun ‘sanitizer’, to amma yanzu duk kun daina. Shin koronar ta tafi ne?
Ka san shi aikin lafiya akwai mataki-mataki. Da ‘guidelines’ yake fitowa. Ita hukumar lafiya ta duniya wato WHO, ita take da alhakin sakin matakan dauka na tursasawa kan wannan koronabairos din. Idan ka lura shekara ta farko da ta biyu babu wani mataki mai sassauci da ya fito daga hukumar lafiya ta duniya, saboda annobar tana kan ganiyarta. Lokacin da aka fara samun sauki sai aka fara saukaka kayyadewa. Misali; masu fita kasashen waje idan ka zo sai an yi maka gwajin korona a tashar jirgin sama an tabbatar ba ka da korona. Aka zo aka fara saukaka kayyadewa, aka ce da zarar kana da sahihin shaidar yi maka allura, zaka iya tafiya. Idan ka je ba ka da bukatar gwajin kana da shi ko baka da shi, wannan shi ne matakin da muke a ciki. Saboda da farko idan ka sauka Nijeriya, idan ka zo kana da bukatar ka cike wasu takardu da zarar ka sauka. Za ka biya kudin gwaji a tashar jirgin saman. Za su kyale ka tafi tare da bibiyar inda kake, sannan idan akwai wani rahoto, cikin sauki za su je wurin su dauke ka zuwa muhallin killacewa. Wannan yana nufin a wancan lokacin korona na kan ganiyarta.
A matakin da muke a yanzu akwai abin da Bature yake cewa; cutar da ake magana a kai akwai allura, an gabatar da allura. Kamar korona, yanzu an gabatar da allurarta. Mutanen da suka zama an yi musu allurar abin da hakan yake nufi shi ne an yi bunkasa abin da ake cewa ‘hard immunity’, idan har akwai wannan matakin kariya din wato ‘hard immunity’ hukumar lafiya ta duniya ba ta da wani zabi illa ta saki wadansu matakai na cikakken kayyadewa ‘as per as issue of corona is concern’. Yanzu a Nijeriya misali ba za mu iya cewa babu koronabairos ba. Amma ko da kuwa akwai koronabairos, shi wanda ya kamu da cutar ba zai zama ‘so sebere, so transient, so communicable’.
Mai karatun zai so ya ji wai shin korota ta tafi?
Toh maganar guda daya ce, zan ba ka amsa tana da harshe guda biyu. Ba za a ce korona ta tafi gaba daya a Nijeriya ba. Harshe na biyu shi ne; akwai kwamiti da shugaban kasa ya kafa, idan ka duba karshen matakan da suka saki ya saukaka kayyadewar da aka sanya na koronabairos. Amma wannan ba yana nufin korona ta tafi baki kaya. Saboda yanzu ko kasashen duniya; akwai abubuwan da ba aiya magana kansa na korona. Amma dai farko kafin a kira akwai batun korona sai ya kasance adadin wadansu mutane sabbin wadanda suka kamu da cutar ne, ka gane? Sai a bayyana fargaba. Amma a yadda take yanzu, tana tsakanin abin da hukumar lafiya ta dunita ta yarje ne na ka’idarta, tana kuma tsakanin abin da kwamitin shugaban kasa kan yaki da korona ya yarje ne. Babu wani abin damuwa. Duukkanin masu ruwa da tsaki akan harkar lafiya suna cikin shiri.
Yanzu kenan a hukumance an daina maganar ‘sanitizer’, an daina wanke hannu don kaucewa korona?
A’a ba cewa aka yi a daina ba. Ai na farko idan ka duba har yanzu idan ka je idan al’umma ke taruwa za ka ga akwai ‘hand sanitizer’ a wajen. Ai ita ‘hand sanitizer’ ba wai korona kadai take magani ba. Misali yanzu cutar kwalara tana yawan shiga da fice. Yanzu misali wannan shi ne lokacin da muke sa ‘Emergency preparedness response system’ namu ‘on cholera’. Saboda da zarar ruwa ya fara sauka saboda dabi’a da muke da shi na bahaya a fili wanda a Abuja ma a bayyane yake. Da zarar an yi ruwa na farko an yi na biyu; duk ya wanke wannan dattin ya tura shi kogi, ka tuna a wannan kogin akwai al’umma wadanda suka dogara da wannan ruwan da shi suke dukkanin ayyukansu na gida. Shi suke girki da shi, shi suke wanki da shi, shi suke duk amfani da shi su dafa abinci. Manoma su suke amfani da shi su wanke karas da salad da ake kawo mana da shi kasuwa.
Wacce shawara za ka bai wa al’ummar Nijeriya dangane da matakan kare kai tunda har yanzu a hukumance ka bayyana mana cewa ba a yi bankwana da koroba ba?
To duk cutar da ta zo alal hakika ta zama da girma kamar korona, yadda ta zo da girma, yadda ta zo da muhimmanci saboda idan ba ka manta ba, akwai lokacin da korona take kan ganiyarta wanda ta tsayar da duniya gaba daya cak waje daya. Jirgin sama ba ya tashi, mota ba ta tashi daga gari zuwa gari, mutane ba sa zuwa kasuwa. Mutane ba sa zuwa masallaci, mutane ba sa zuwa ko’ina. Sai duniya ta tsaya cak, to lallai wannan cuta tana da abin da ake ce mata ‘public Health importance’. Saboda haka ba abin wasa bane, duk abubuwan da aka ce an kayyade an yi hakan ne ‘with modesty’. Yanzu misali duk wanda ya san mene ne illar korona, ba zai zo inda akwai cunkuso ya je ya zauna ba. Ko kuma ya ga ana tari, ko kuma ya ga mutane na atishawa sannan ya tsaya kusa da su. Za ka ga har yanzu tsofaffi ko kuma wanda suke da ‘predisposing element’ kamar Diabeties, Heypertension, Tuberculosis da kuma ‘other respiratory tract infections’ za ka ga duk inda za su je suna sa ‘face mask’ har gobe. Duk wadannan kana daukar matakai ne tare da nuna cewa korona ba ta tafi ba. Saboda idan ka duba kamar kasashe irin su Indiya, su Amurka, da wasu bangare na Turai, har yanzu suna kawo rahoton cutar korona har yanzu a asibiti. Ba za a ce ta tafi ba.
To kiran da muke yi ma al’umma duk abin da suka sani suna yi da na kariya su ci gaba da yi, sannan abu mafi muhimmanci kowa ya tabbatar da cewa ya je ya karbi rigakafin korona. Saboda idan ka karbi wannan rigakafin korona din zai taimaka. Ba wai ana cewa idan ka karbi rigakafi ba za ka yi korona ba ne, a’a ko da korona za ta kama ka za ta zo da sauki.
Mun gode
Nima na gode